Ad 0123

download Ad 0123

of 336

Transcript of Ad 0123

GARDANCIN HAUSAWA JIYA DA YAU

BY ABDULRAHAMAN ADO

MASTER OF ARTS (HAUSA STUDIES)DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES

USMANU XANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO(POSTGRADUATE SCHOOL)

JANUARY, 2009

1

USMANU XANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO(POSTGRADUATE SCHOOL)

GARDANCIN HAUSAWA JIYA DA YAU

A dissertation Submitted to the Postgraduate school

BY ABDULRAHAMAN ADO

In partial fulfillment of the requirements for the award of the Degree of MASTER OF ARTS (HAUSA STUDIES)

DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES

JANUARY, 20092

SADAUKARWA Ni Abdulrahaman Ado Malumfashi, ina mai matuqar farin cikin sadaukar da wannan aiki na bincike wanda aka gabatar da shi ga Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jamiar Usmanu Xanfodiyo Sakwwato, ga mahaifana Alhaji Ado Muhammadu Malumfashi da kuma Hajiya Mariya Malumfashi (Allah Ya gafarta masu).Waxannan mahaifa nawa su ne suka xauki xawainiyar tarbiyyata har na kawo zuwa yanzu, Allah Ya jiqansu da gafararsa, ya kuma saka masu da Aljannar Firdausi, Amin.

3

CERTIFICATION

This Dissertation by ABDULRAHAMAN ADO (ADM. NO. 05211106011) has met the requirement for the award of the Digree of Master of Arts (Hausa culture) of the UsmanuXanfodiyo University, Sokoto and is approved for its contribution to knowledge.. Prof. A.M. Bunza Main Supervisor Date. . Dr. B.B. Usman Co-Supervisor i Date.. Prof. Yanxaki A. Co-Supervisor II Date.

.Dr. A.H. Amfani Head of Deparment Date Prof. A.Y. Bichi External Examiner (Chairman of the Panel)

Date.Date of Examination.

4

GODIYA Dukkan godiya ta tabbata ga Sarki Allah (SWT), sannan tsira da amincin Allah su tabbata bisa ga shugabanmu kuma annabinmu, Annabi Muhammadu xan Abdullahi, wanda ya kawo mana shiriya da ilimi da bisirar zaman duniya da lahira a cikin Alqurani mai girma. Haka kuma, ina mai qara miqa godiya ga Allah (SWT), wanda ya nufe ni da rabon kammala wannan aiki, cikin qoshin lafiya, duk da ximbin matsalolin da na dinga cin karo da su, tun lokacin da na aza harsashin son yin digiri na biyu, a fannin ilimin koyarwa a shekarar 2001/2002 da kuma a fannin nazarin Hausa, a shekarar 2005/2006. Allah, na gode qwarai da, a yau, Ka ba ni ikon yin digiri na biyu a kan sanaar gardanci a qasar Hausa mai take: Gardancin Hausawa Jiya Da Yau. Ina kuma roqonKa gafara, da ka yafe mani duk wasu kurakurai, waxanda na tafka a cikin wannan aiki, domin aiki ne da ya tavo harkar ilimin addinin musulunci. Ina miqa godiya ta musamman ga jagororin wannan aiki nawa. Da farko, akawi Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza, wanda shi ne ya ba ni qarfin guiwar yin bincike a wannan fanni, ya kuma ci gaba da gwarzanta ni a lokacin da nake yin rubutun aikin. Shi kuwa Dakta Bello Bala Usman, ya fito mani da gyare-gyren da ya kamata a yin a wannan aiki, tun daga farkon shafi har zuwa na qarshe. Farfesa Aminu Yanxaki kuwa ya fito da wasu alamurra waxanda ya ga babu su a cikin wannan aiki, ya5

kuma bayar da umurnin sanya su. Hasali ma, shi ne ya sa aka sanya wani karin maganar da yake cewa: Kura ma ci tilawar gardi. Allah Ya saka maku da alherinsa, amin! Godiya mai tarin yawa nake sake miqawa ga malaman da suka koyar da ni, sannan kuma suka taimaka mani da littattafan da na yi amfani da su a wajen gudanar da wannan aiki. Wasu daga cikinsu sun haxa da Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza da Dokta Ahmed Amfani da Dokta Atiku Dunfawa da Dokta Ibrahim Malumfashi da Dokta Salisu Yakasai da Mallam Habibu Sani Vavura( na Jamiar Bayero ta Kano) da sauran Malaman Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jamiar Usmanu Xanfodiyo, Sakkwato. A wajen miqa godiya ta, ba zan so in manta da mutanen da suka taimaka mani ba a wajen harkar ilimin da na samu na naura mai qwaqwalwa, wanda na yi amfani da shi na buga wannan aiki, kuma a sanadiyyar haka na zauna jarrabawar kwamfuta(naaura mai

qwaqwalwa), kuma na ci. Waxannan kuwa sun haxa da Mrs. B. O. Ijasan(Principal FGC Sokoto) da Mr. O., Gerald da Mr.A., Dada da Hausa Business Centre da Umar Garkuwa da sauran waxanda suka taimaka. Daga qarshe, ina miqa godiya ta ga Mallam Mukhtar Xanbini, wanda ya xaukar mani duk hotunan da aka yi amfani da su a rataye. Sai kuma godiya ga duk waxanda suka yarda aka yi hira da su,suka kuma ba6

ni bayanai waxanda aka yi amfani da su a wannan kundi na bincike. Kaxan daga cikinsu sun haxa da: Mallam Isa Abubakar da Alhaji Amadu Nalado da Alhaji Garba Nakande da Alaramma lukman Malumfashi da Jamilu Tela da Mallam Salisu Audi Mabera da Alaramma Auwal Ahibba da Mallam Umar mai almajirai Mabera da mallam Lawal mai kura da duk waxanda sunansu ya fito a jerin waxanda aka yi hira da su. Allah ya saka maku da alherinsa. Amin!

7

TSAKURE Taken wannan bincike shi ne Gardancin Hausawa Jiya Da Yau. Gardanci sanaa ce ta nuna bajinta da bayar da magunguna, wadda ake yin amfani da ilimin addinin musulunci da na gargajiya. A cikin wannan kundi an yi bitar ayyukan da suka gabata masu alaqa da gardanci da hujjojin ci gaba da bincike da manufar bincike da wahalhalun aka ci karo da su a wajen bincike da kuma iyakancewar bincike. An kuma kawo asalin samuwar sanaoin gargajiya da alaqarsu da sanaar gardanci a qasar Hausa, kafin da bayan zuwan baqi da asalin samuwar kalmar gardi da sanaar gardanci. An kuma kawo fasalin sanaar gardancin dabbobi da na karatu da na wando da na a-dak-buzu da bayani a kan matsayin sanaar gardanci a zamanin yau na zuwan Turawa da yawaitar ilimin addinin musulunci.

8

ABSTRACT The title of this work is Gardancin Hausawa Jiya Da Yau. It is a research work on Hausa traditional occupations that provides human medicines, done by us of bravery and Islamic knowlege. The work contained the meaning and origin of gardanci traditional occupation, a review of releted literatures, reasons for further studies, aims and objectives of the study, difficulties encountered during the reasearch and scope of the study. The history of the origion of traditional occupations in Hausa land and their relationship with gardanci, before and after the coming Islam and Europeans and, the origin of the words gardi and gardanci has been explained. Finanly, the effects of the present day modernization ( ie the coming of Europeans and expantion of Islamic knowledge), on the Gardanci occupations in Hausa land was discussed

9

ABUBUWAN DA KE CIKI Taken Bincike Sadaukarwa Certification Godiya Tsakure Abstract Abubuwan da ke ciki i ii iii iv vii viii ix

BABI NA XAYA 1.0 Gabatarwa 1.1 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata. 1.2 Hujjar Ci Gaba Da Bincike 1.3 Manufar Bincike 1.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike 1.5 Kayan Da Aka Yi Amfani Da Su Wajen Yin Bincike 1.6 Matsalolin Bincike 1.7 Iyakancewar Aiki 1.8 Naxewa 1 5 18 22 26 30 31 35 35

BABI NA BIYU Tarihin Samuwar Sanaoin Gargajiya A Qasar Hausa 2.0 Ta Da Alaqarsu Da Sanaar Gardanci 2.1 Asalin Samuwar Sanaoin Gargajiya Na Hausa A Qasar Hausa Kafin Zuwan Musulunci 2.2 Hanyoyin Nuna Gwaninta A Cikin Sanaoin Hausawa Na Gargajiya Kafin Zuwan Musulunci 2.3 Dangantakar Sanaoin Hausawa Na Gargajiya Da Sanaar Gardanci A Qasar Hausa Kafin Zuwan Musulunci 2.4 Sanaoin Hausawa Na Gargajiya Bayan Zuwan Musulunci 2.5 Hanyoyin Nuna Gwaninta A Cikin Sanaoin Gardanci Da Kuma Sauran Sanaoin Hausawa Na Gargajiya Bayan Zuwan Musulunci Qasar Hausa 2.6 Tasirin Sanaar Malanta A Kan Sanaar Gardanci Da Sauran Sanaoin Gargajiya Na Hausa 2.7 Dangantakar Sanaoin Gargajiya Na Hausa Da Sanaar10

36 37 45 54 58 65 70

Gardanci Bayan Zuwan Musulunci Qasar Hausa 2.8 Sanaoin Hausawa Na Gargajiya Bayan Zuwan Turawa Qasar Hausa 2.9 Sanaar Gardanci A Qasar Hausa Bayan Zuwan Turawa 2.10 Naxewa BABI NA UKU

76 77 79 81

3.0 Tarihin Asalin Samuwar Kalmar Gardi Da Sanaar GardanciA Qasar Hausa 82 3.1 Asalin Kalmar Gardi Da Sanaar Gardanci Daga Zabarmawa 83 3.2 Asalin Kalmar Gardi Da Sanaar Gardanci Daga Farauta 86 3.3 Asalin Kalmar Gardi Da Sanaar Gardanci Daga Barebari ( Ko Barno) 94 3.4 Asalin Kalmar Gardi Da Sanaar Gardanci Daga Almajiranci (Neman Ilimin Addinin Musulunci) 99 3.5 Taqaitaccen Tarihin Asalin Samuwar Sanaar Gardanci A Qasar Hausa 105 3.6 Naxewa 114 BABI NA HUXU 4.0 4.1 Fasalin 116 Sanaar Gardancin Dabbobi A Qasar Hausa

Sanaar Gardancin Kuraye 117 4.1.1 Garuruwan Da Aka Fi Yin Sanaar Gardancin Kuraye 118 4.1.2 Yadda Aka Fara Gudanar Da Sanaar Gardancin Kura A Qasar Hausa 121 4.1.3 Yadda Ake Gudanar Da Sanaar Gardancin Kuraye 126 4.1.4 Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su A Wajen Sanaar Gardancin Kuraye 133 4.1.5 Amfanin Sanaar Gardancin Kuraye Ga Alummar Hausawa 134

11

4.1.6 4.2

Haxurran 140

Da Sanaar

Ke

Cikin

Sanaar Gardancin

Gardancin

Kura Biri.

141 4.2.1 Garuruwan Da Aka Fi Yin Sanaar Gardancin Biri 143 4.2.2 Yadda Aka Fara Gudanar Da Sanaar Gardancin Biri A Qasar Hausa 144 4.2.3 Yadda Ake Gudanar Da Sanaar Gardancin Biri A Qasar Hausa 145 4.2.4 Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su Wajen Gudanar Da Sanaar Gardancin Biri 150 4.2.5 Haxurran Da Ke Cikin Sanaar Gardancin Biri 151 4.2.6 Amfanin Sanaar Gardancin Biri Ga Alummar Hausawa 152 4.3 Sanaar Gardancin Macizai 154 4.3.1 Garuruwan Da Aka Fi Yin Sanaar Gardancin Maciji 155 4.3.2 Yadda Aka Fara Gudanar Da Sanaar Gardancin Macizai A Qasar Hausa 156 4.3.3 Yadda Ake Gudanar Da Sanaar Gardancin Macizai A Qasar Hausa 160 4.3.4 Kayan Yin Sanaar Gardancin Macizai 177 4.3.5 Haxurran Da Ke Cikin Sanaar Gardancin Macizai 178 4.3.6 Amfanin Sanaar Gardancin Macizai 179 4.4 Sanaar Gardancin Kunama 179 4.4.1 Garuruwan Da Aka Fi Yin Sanaar Gardancin Kunami 180 4.4.2 Yadda Aka Fara Sanaar Gardancin Kunami 182 4.4.3 Yadda Ake Gudanar Da Sanaar Gardancin Kunami 18212

4.4.4 Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su A Wajen Gudanar Da Sanaar Gardanci 184 4.4.5 Haxurran Da Ke Cikin Sanaar Gardancin Kunami

Kunami

185 4.4.6 Amfanin Sanaar Gardancin Kunami Ga Alummar Hausawa 185 4.4.7 Naxewa 186 BABI NA BIYAR 5.0 Fasalin Sanaar Gardancin Karatu Da Na Wando Da Na A-Daki-Buzu 187 5.1 Gardancin Karatu 188 5.1.1 Matakan Karatun Alqurani Na Zama Gardi A Qasar Hausa 190 5.1.2 Garuruwan Da Aka Fi Yin Sanaar Gardancin Karatu 200 5.1.3 Yadda Aka fara Gudanar Da Sanaar Gardancin Karatu A Qasar Hausa 201 5.1.4 Yadda Ake Gudanar Da Sanaar Gardancin Karatu 203 5.1.5 Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su A Wajen Gudanar Da Sanaar Gardancin Karatu 206 5.1.6 Haxurran Da Ke Cikin Sanaar Gardancin Karatu 208 5.1.7 Amfanin Sanaar Gardancin Karatu Ga Alummar Hausawa 213 5.2 Gardancin A-Daki-Buzu 215 5.2.1 Garuruwan Da Aka Fi Yin Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu 216 5.2.2 Yadda Aka Fara Yin Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu 217 5.2.3 Yadda Ake Gudanar Da Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu A Qasar Hausa 217 5.2.4 Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su A Wajen Gudanar Da13

Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu 221 5.2.5 Haxurran Da Ke Cikin Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu 221 5.2.6 Amfanin Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu Ga Alummar Hausawa 222 5.3 Gardancin Wando 224 5.3.1 Garuruwan Da Aka Fi Yin Sanaar Gardancin Wando A Qasar Hausa 225 5.3.2 Yadda Aka Fara Gudanar Da Sanaar Gardancin Wando A Qasar Hausa 226 5.3.3 Yadda Ake Gudanar Da Sanaar Gardancin Wando A Qasar Hausa 231 5.3.4 Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su A Wajen Gudanar Da Sanaar Gardancin Wando 241 5.3.5 Haxurran Da Ke Cikin Sanaar Gardancin Wando 245 5.3.6 Amfanin Sanaar Gardancin Wando Ga Alummar Hausawa 247 5.3.7 Naxewa 251 BABI NA SHIDA. 6.0 253 6.1 Tasirin Zamani A Kan Sanaar Gardancin Dabbobi 254 6.1.1 Canje-Canjen Da Sanaar Gardancin Dabbobi Ta Samu A Sanadiyyar Zuwan Turawa 254 6.1.2 Canje-Canjen Da Sanaar Gardancin Dabbobi Ta Samu A Sanadiyyar Yawaitar Ilimin Addinin Musulunci 259 6.2 Tasirin Zamani A Kan Sanaar Gardancin Karatu 26114

Matsayin

Sanaar

Gardanci

A

Yau

6.2.1 Canje-Canjen Da Sanaar Gardancin Karatu Ta Samu A Sanadiyyar Zuwan Turawa 261 6.2.2 Canje-Canjen Da Sanaar Gardancin Karatu Ta Samu A Sanadiyyar Yawaitar Ilimin Addinin Musulunci 264 6.3 Tasirin Zamani A Kan Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu 265 6.3.1 Canje-Canjen Da Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu Ta Samu A Sanadiyyar Zuwan Turawa 266 6.3.2 Canje-Canjen Da Sanaar Gardancin A-Daki-Buzu Ta Samu A Sanadiyyar Yawaitar Ilimin Addinin Musulunci 267 6.4 Tasirin Zamani A Kan Sanaar Gardancin Wando 269 6.4.1 Canje-Canjen Da Sanaar Gardancin Wando Ta Samu A Sanadiyyar Zuwan Turawa 270 6.4.2 Canje-Canjen Da Sanaar Gardancin Wando Ta Samu A Sanadiyyar Yawaitar Ilimin Addinin Musulunci 270 6.5 Naxewa 272 Littattafan Da Aka Duba 273 Mutanen Da Aka Yi Hira Da Su 280 Rataye 285

15

XAYA. BABI NA XAYA. 1.0 GABATARWA Hausawa na cewa: gardanci taqamar biri ce, kowa da yadda yake taka tasa. Abin nufi anan shi ne, kalmar gardanci, kalma ce mai faxi, wadda maanarta ta tana da yawa, to amman duk ana iya tara su, a tace su zuwa kashi biyu, kamar haka: Farko dai, maanar kalmar gardanci ta haxa da duk wani mutum mai yin wasa da dabbobi, irin su kura, da biri, da maciji, da sayaki da dila da kunami (Ango,2000:21 ), ko kuma duk wani mutum mai yin amfani da hanyar almajiranci (wato ilmin addinin musulunci), don tunkarar wani abu mugu (mai rai ko mara rai), ya kuma iya sarrafa shi (wasa da shi), ta yadda ya ga dama, sannan ya bayar da magungunan waraka daga ciwon da wannan abu kan iya haddasawa.1 Ke nan, ta wannan hauji na farko, sanaar gardanci na nufin, sanaa ce ta iya tunkarar wani abu mugu, wanda ake jin tsoronsa ko ake shakkarsa, a kuma iya sarrafa wannan abu ta yadda aka ga dama, da kuma iya bayar da maganin dafinsa, idan abin ya cutar da mutum, ko kuma bayar da maganin yin rigakafin abin tun kafin ya kai ga cutarwa. Hausawa dai na cewa : rigakafi, ya fi magani. Bugu da qari, mallakar asirai na waibuwa (buwaya), daga Alqurani mai girma ne ke sanya irin

1

Hirar Da Aka Yi Da Mallam Isa Abubakar, Sarkin Gardin Sarkin Musulmi, Qofar Rini, Sakkwato.

16

waxannan mutane (gardawa), masu yin wannan sanaa ta gardanci, ke iya tunkarar duk wani abu mugu, su kuma iya sarrafa shi, ta yadda suka ga dama. Irin mugayen abubuwan kuwa sun haxa da, kura, da sayaki, da biri, da maciji, da kunama, da kaifi (watau kamar wuqa, da takobi, da lauje, da adda), da tsini (irin su mashi, da qaho), da kuma sanda ko tsumagiya.2 (Nasasawa,1977:10). Maana ta biyu kuwa ita ce wadda ke nufin gardi(mai yin sanaar gardanci) a matsayin saurayi wanda hannunsa ya nuna wajen iya rubutu, kuma ya yi ido sosai, yana karanta Alqurani babu kuskure (Nasarawa, 1997:7). Ko kuma xalibi wanda ba shi da mata(kura), wanda ya girma, ya san ciwon kansa, wanda ya kai kimanin shekara ashirin da biyar, har zuwa sama (Ango,2ooo:21 da Abubakar,2002:54 da Barkum, 1990:51 da Sarari,1989:37). Saboda haka, sanaar gardanci sanaa ce ta ilimi da nuna bajinta3, wadda ta samo tushe a sanadiyyar farauta (Nasarawa,1997:9), wadda kuma daga baya, aka cakuxa ta da ilimin addinin musulunci (Garba,1991: 104 ) . Ilimin kuma na tsibbu ne, domin Nasarawa,(1997:10), ya ce: Irin taimakon da [gardawa]su kan samu, ya haxa da na wasu ayoyi daga Alqurani. Bayan sun sami wannan taimako sai kuma su haxa su da wasu surkulle kamar ta amfani da laya, karhu ko guru, kamar yadda wasu ke kiransa.

2 3

Hirar Da Aka YI Da Mallam Muhammadu Voyi, Sarkin Gardin Arxon Shuni, Sakkwato. Hirar Da Aka Yi Da Mallam Muhammadu Umaru, Sarkin Gardin Yabo, Sakkwato.

17

Kusan duk masu yin sanaa ta gardanci malamai ne. Babu gardi, xan asali (wanda ya yi gado), wanda ba shi da ilimin addinin musulunci. Hasali ma, yaren(karin harshen ko zaurance) gardanci (watau toganci), wanda gardawa (jamin gardi), suke yin amfani da shi, domin yin magana da juna (don su iya gane juna), su kuma vatar da bami, a cike yake da kalmomin larabci, wanda sai mai ilimin addinin musulunci ne kawai zai iya fahimtarsa, da gane shi.4 (Sarari, 1989:36-38).(A duba shafi na 250251 a ga misalin zaurancen gardawa). Illa iyaka, alamarin gwamutsa alada da addinin musulunci, a wajen Bahaushe, sanannen abu ne kuma daxaxxe(Ibrahin,1982:89). Zarruk(1986:33) ma ya ce : Bayan karvar addinin musulunci, sai ya kasance Hausawa suna gwama aladunsu na maguzanci da kuma irin na addinin musulunci. Haka kuma, Bunza(2001:92), ya qara da cewa : Bayan da Hausawa suka karvi addinin musulunci, suka ilimantu a ciki sosai, suka cuxanya wasu dabarun magungunansu da na waraka cikin na musulunci, aka samu magungunan tsibbu Bincike ya nuna cewa, dalilai biyu ne kan sanya gardi(mai yin sanaar gardanci) danganta kansa da malamai. Da farko dai, gardi almajiri ne wanda ya koyi ilimin addinin musulunci, har ya kai ga matakin mallam. (Abubakar,2002:54 da Barkum, 1990:51-53). Na biyu kuwa, don neman qimanta sanaarsa, sai ya danganta ta da sanaar da ta riga ta sami4

Hirar Da Aka Yi Da Mallam Modi Kwakwata, Sarkin Gardin Dancaxi, Sakkwato.

18

qima da daraja a idon jamaa (watau malanta), don gudun kada a raina masa ita (Zarruq,1986:50). Ibrahim(1982:301) ma ya ce: . Bahaushe ya ci gaba da girmama da darajanta malamai kamar yadda ya saba yana girmama shugabannin addininsa na gargajiya. Irin wannan muqami da aka bai wa malamai sai ya sa wasu daga cikinsu suka xauki xabia irin ta shugabannin addinin gargajiya watau bokaye da yan bori. Amma kuma, ana danganta gardi a matsayin malamin tsibbu, domin kusan duk ayyukan sanaarsa ta yan tsibbu ce, kamar yadda Bunza (2001:92), ya kawo maanar tsibbu, da cewa : A wasu lokuta, ana nufin dabo, ko sihiri, ko siddabaru.A wani lokacin,takan xauki maanar yaudara da zalunci, da cuta, da damfara, da qwaruwa da dai makamantansu. A wani lokaci, tana xaukar maanar wayo, da dabara, da walankeluwa, da dibilwa, da ire-irensu. Kamar yadda Bunza ya yi bayanin maanar tsibbu, haka ma masu yin sanaar gardanci, waxanda Mallam Habibu Sani Vavura,5 ya kira da sunan yan dabo, sukan yi amfani da ilimin addinin musulunci, da na gargajiya, domin yin dabo, da rufa ido, da sihiri, da siddabaru ko wayo da dabara, da walankeluwa, da dibilwa da dai sauran irinsu, a wajen gudanar da sanaarsu ta gardanci, kamar a wajen yin wasa da dabbobi irin su kura, da sayaki, da biri, da maciji, ko a wajen gwada taurin gardawa na wuqa ko hawa mashi ko hawan qaho ko shuka duma, ya yi tsiro, ya girma har ya kai ga yin yaya, ko kuma yin kara-karan gardawan karatu ko dabonHirar Da Aka Yi Da Mallam Habibu Sani Vavura, Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jamiar Bayero, Kano.5

19

kuxi, da dai sauransu barkatai, kamar yadda za a gani a cikin wannan kundi na bincike.

1.1.

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA. Mallam Umaru Mana ya ce, masu hikima na cewa: gardanci,

taqamar biri ce, kowa da yadda yake taka

tasa.6 Ke nan, sanaar

gardanci, sanaa ce sha-kundum, ko kuma kalma ce mai faxi (wadda ta haxa da yin abubuwa da yawa) waxanda Hausawa ke gudanarwa ta yin amfani da asirran da suka samo daga sanadiyyar koyon ilimin addinin musulunci (karatu da rubutu) da kuma tambayoyi na siddabarun gargajiya (Nasarawa,1997:9) da ke da tushen ko alaqa da iskoki (aljanu). Saboda haka, bitar da aka gabatar a wannan kundi, na ayyuka ne da suka gabata, waxanda suka danganci sanaar gardanci, da malanta ko almajiranci, da magungunan gargajiya da suka danganci tsibbu, da siddabaru, da dabo (ko rufa ido), da tashen almajirai ko malamai, da tauri (irin na gardawa), da irin ayyukan bajinta da masu sanaar gargajiya kan nuna, waxanda suka yi kama da na gardanci (kamar na yan hoto), da dai makamantansu. Bugu da qari, yin bitar ayyukan da suka gabata na sanaar malanta da almajiranci ya zama wajibi, domin sanaar gardanci (na karatu), wani mataki ne na almajiranci da malanta, wanda, wasu na ganin daga gare su ne sanaar gardanci (na karatu da na wando da na6

Hirar Da Aka Yi Da Mallam Umaru Mana, Sanqiran Unguwar Mana Da Tamaje, Sakkwato.

20

kuma a-daki-buzu) suka samo tushe. Wani Mawaqi mai suna Bala Mila, na cewa : Daxin duniya yakan iya ruxa samari, Daxin duniya mai mai da musulmai kafirai Haka kuma, Hausawa na cewa : Shagalin duniya, Mai sanya malami da allonsa, Ya haye ya bar buzunsa.. Abin nufi a nan shi ne, samun duniya (watau jin daxi), kan iya sanya mutum musulmi, mai ilimim addinin musulunci (ko ma malami ko almajiri), ya fanxare, ya bar hanyar karatu, ya bi shagalin shexan na duniya. Bitar da aka yi ta kasance kamar haka: Abubakar, M.I. (2002), ya kawo bayani a kan maanar gardi, da matakan zama gardi, da matakan koyon karatu na gardi, da maanar karin harshen gardawa, da ire-iren karin harshen gardawa, da kuma hikimar da ke cikin karin harshen gardawa. Yin bitar wannan aiki zai sanya a qara gasganta cewar gardawa suna da karin harshe wanda suke yin amfani da shi a lokacin wasanninsu na gardanci, ba ma kamar na gardin wando, sukan yi amfani da toganci, wanda karin harshe ne mai cike da kalmomin larabci (a duba shafi na 250-251 a ga misali na Karin harshen gardawa).Sai dai wannan aiki ba cikakken aiki ba ne akan dukkan sanaar gardanci.Ya dai tavo gardancin karatu,amman bai ce komai ba akan

21

sauran sanaoin gardanci ba kamar na wando da na a-daki-buzu da na dabbobi. Alhassan, H. Da Wasu (1982), sun fito da nazari a kan sanaoin Hausawa na gargajiya guda ashirin da biyar, a cikin babuka guda biyu, watau babi na biyar da na shida. A cikin waxannan sanaoi, sanaar farauta, da ta malanta, da kuma ta maganin gargajiya ce kawai ta shafi wannan aiki. A sanaar farauta, ya bayyana maanar farauta, da yadda ta samo asali, da hanyoyin gudanar da farauta, da kuma iri shirye-shiryen da ake yi kafin a fita farauta.Ta fannin malanta kuwa, marubucin ya kawo maanar malanta, da ire-iren malantar gargajiya, da yadda ake tafiyar da sanaar malanta, da kuma muhimmancin malanta ga alummar Hausawa. Ita kuwa sanaar maganin gargajiya, marubucin ya fara da kawo maanar maganin gargajiya, da ire-iren magungunan gargajiya da suka qunshi tsime da sassaqe-sassaqe da turare da qulle-qulle, da tofawa, da shafawa, da gashi da jiqe-jiqe da jifa da ajiya da rataye da siddabaru da kuma shashatau. Daga qarshe kuma, sai marubucin ya kawo muhimmacin sanaar maganin gargajiya ga alummar Hausawa. Bugu da qari, a babi na takwas, wanda aka yi wa taken; Ana Bikin Duniya, marubucin ya yi bayani a kan dabo. A nan ya kawo ire-iren dabon da Hausawa kan yi, kamar su dabon wasan kwaikwayo, da dabon gardawa, da dabon yan damfara, da dabon yan walawala, da dabon zamba cikin aminci, da kuma dabon xauki-ka-ba-ni. A dabon gardawa, wanda shi ne ya shafi wannan22

aiki, marubucin ya kawo bayanai na irin dabarun da mai yin sanaar gardanci ke aiwatarwa na waibuwa, a dandali, a lokacin da yake aiwatar da sanaarsa. Yin bitar wannan littafi, zai zama kamar wata hanyar da za a fasalta yadda sanaar farauta take, wadda marubuta da dama, irin su Ango [2000], ke kallonta a matsayin sanaar da gardanci ta samo tushe, tun kafin zuwan addinin musulunci. Haka kuma, nazarin da aka yi, na malanta, zai taimaka wajen sanin yadda malanta take gudana, domin ana ganin cewa, sanaar malanta ce ta haifar da ci gaban sanaar gardanci, bayan zuwan addinin musulunci, a lokacin da xalibai ke son zama malamai. Bugu da qari, bitar magungunan gargajiya, zai sanya a san irin magungunan da gardawa kan bayar a matsayin taimako, ga alummar Hausawa. Daga qarshe, bitar wannan littafi, za ta fayyace ire-iren dabon da gardawa kan yi a dandali, a lokacin wasannin sanaarsu ta gardanci. Ke nan, wannan littafi yana da dangantaka da wannan aiki, sai dai, in banda almajirancin karatun Alqurani da ya yi magana, bai fayyace irin gardawan da kan yi dabon da ya yi bayani ba. Ango, H.M. (2000), ya kawo bayanai a kan almajiranci, wanda ya fid do da fasalin almajirai, da makarantun allo, da kuma yadda ake gudanar da karatun allo a garin Sakkwato. A wajen bayanin da ya yi na rabe-raben almajirai, ya kasa matakan yin ko gudanar da karantun allo zuwa gida uku. Akwai matakin kotso, da na titiviri, da na gardi. Haka kuma, marubucin ya kawo bayanin maanar gardanci, da kuma ire23

iren gardawa. Ya bayyana cewa, baya ga gardi, wanda yake almajiri ko xalibi, wanda ba ya da mata, da gardi mai kura (mata), ya kuma kawo xan taqaitaccen bayanin gardi mai wasa da dabbobi, irin su kura da biri da maciji.Wannan marubuci ya yi aikinsa ne a kan almajiranci a garin Sakkwato kawai. Wannan kila shi ya sa bai iya kawo cikakken bayanai ba a kan matakan da almajiri kan hau ya kai ga matakin gardi da kuma na gaba da gardi ba. A maimakon matakai guda tara na almajiranci(watau molo da qolo da valla da gardi da mallam da alaramma da gwani da gangaram), sai ya kawo uku kawai(watau kotso da titiviri da gardi). Haka kuma, a fanning gardancin dabbobi, marubucin ya ambaci sunayen gardawan kura da biri da maciji kawai, amma bai yi wani bayani ban a yadda suke da yadda ake gudanar da sanaarsu da garuruwan da aka fi samunsu da amfaninsu da haxurran da ke tattare da sanaar. Hakazalika, duk da cewa a garin Sakkwato aka yi wannan bincike, marubucin bai ce uffan ba a kan gardawan wando da na a-daki-buzu, wanda aka fi samu a Sakkwato. Ken an, wannan aiki taqaitacce ne. Saboda haka, aikin Ango(2000), yana da bambanci da wannan aiki na Gardancin Hausawa Jiya Da Yau, Shi dai Ango(2000) ya yi aikinsa ne a taqaice a kan almjiranci a garin Sakkwato, amman wannan kundi an yi shi ne a faxaxe, wanda ya qunshi cikakkun bayanai na dukkan gardancin Hausawa guda bakwai( watau na kura da na biri da na maciji da na kunama da na karatu da na wando da kuma na a-daki-buzu). Haka kuma ba a garin Sakkwato24

binciken ya tsaya ba, ya kalwaxe dukkanin qasashen Hausa da ke a arewacin Nijeriya. Barkum, I.M. (1990), ya kawo bayanai a kan rabe-raben malamai a qasar Hausa. A cikin rabe-raben ya kawo wani bayani a kan wani kaso na gardawa masu yin sanaar gardancin karatu. Har ila yau, a cikin gardawan karatu, ya sake fito da wani kaso na gardi sak, wanda shi ne xalibi wanda ya mallaki hankalinsa, kuma yakan tashi daga gari zuwa gari domin neman karatu. Sai kuma gardi mai kura, wanda shi ne wanda yake tafiya wajen yawon karatu tare da matarsa. Bitar wannan kundi an yi shi ne domin a sami qarin fahimta ta ire-iren gardawan karatu a qasar Hausa, domin mutane da dama, da aka yi hira da su, suna ganin kamar sanaar gardanci, ta samo tushe ne daga almajiranci. Haka kuma, kundin an yi nazarinsa domin a gaskanta cewa, ba a wuri xaya ne almajiri kan sami naqullan da zai tafiyar da sanaarsa ba, yakan yi yawo daga gari zuwa gari. Wannan shi ne kan sa gardi yin yawo daga gari zuwa gari, don tafiyar da sanaarsa.Wannan littafi yana da dangantaka da wannnan aiki ta fannin gardancin karatu.Amma marubucin bai kawo wani bayani ba akan gardancin dabbobi da na wando da na a-daki-buzu ba. Bunza, A.M.(1999), ya yi bayani a kan kore da yan kore, da irin rawar da suke takawa a dandali. Bayaninsa ya yi daidai da yadda gardawan wando da na dabbobi, da na macizai ke yin amfani da kore da yan kore, a lokacin da suke gudanar da sanaarsu, a dandalin25

kasuwa ko na unguwanni, da qauyuka. Malamin ya fara kawo maanar kore, sannan sai ya kawo bayanai na dalilan da kan sa masu wasa a dandali kan yi amfani da yan kore. An yi bitar wannan aiki ne domin a fahimci cewa, gardi, wanda kan yi wasansa a dandalin kasuwa ko wani wurin yin wasa, to shi ma yakan yi amfani da yan kore, a wajen gudanar da sanaarsu, ta gardanci.Dangantakar da wannan maqala ke da ita da wannan aiki, bai wuce ta yin amfani da yan kore ba, wanda wasu masu sanaar gardanci kan yi a lokacin sanaarsu ta gardanci.Ba ma kamar irin su gardawan dabbobi da na wando. Bunza, A.M. (2004), ya kawo bayanai a kan tsibbu, da asalin yadda tsibbu ke farawa, da kuma inda masu tsibbu ke tsinto asirransu, wanda suke amfani da su a wajen tafiyar da harkar sanaarsu. Da yake, ana ganin kamar daga karatun allo ne akan yi tazarce zuwa sanaar gardanci, kuma ana kallon gardi a matsayi xan tsibbu, saboda yadda yake yin amfani da ilimin gargajiya da ma musulunci a wajen bayar da magungunansa na taimako.Saboda haka an yi bitar wannan maqala, domin a fahimci bayanin yadda sanaar gardanci take da danganci tsibbu. Xangambo, A. (1984), ya kawo wani xan taqaitaccen bayani a kan gardawa na yan a-daki-buzu. A cikin bayaninsa, ya fayyace gardawan a-daki-buzu, a matsayin makaxan malamai, waxanda ke gudanar da wasansu ta hanyar bugun buzu da yin rawa. Wannan rawar ce ke sa a sami dariya da raha, domin ganin yadda gardi, wanda yake dattijo, ke26

dagewa yana dukan buzu, yana tsalle, yana rawa, yana waqa, yana juyi, tare da matansa da yayansa. Bitar wannan xan qaramin littafi zai gaskanta cewa, a cikin rukunnan masu sanaar gardanci, akwai waxanda ake kira gardawan a-daki-buzu. Domin, su gardawan a-daki-buzu, a yanzu ba a ganinsu suna wasa. Idan ka faxa ma wanda bai san su ba, cewar akwai irinsu, yana iya qaryatawa. To, amman ganin an kawo bitar su, zai sanya duk wanda ya yi nazarin wannan aiki, zai gaskanta cewa, lallai akwai irinsu ko an tava yin irinsu, a qasar Hausa.Duk da cewar wannan marubuci ya kawo taqaitaccen bayani akan gardawan a-dakibuzu, bai ce komai ba akan sauran gardawan qasar Hausa. Garba, C.Y. (1991), ya kawo tsibbu a matsayin sanaar gargajiya, sannan kuma ya kawo bayanain hanyar da ake bi ana koyon tsibbu. Haka kuma, marubucin ya yi bayani a kan hanyar da almajirai kan bi, domin samun irin asiransu da suke amfani da su a wajen gwada ayyukansu na waibuwa. Kamar yadda bayanai suka gabata, cewa akan yi bitar ayyukan da suka shafi tsibbu, saboda ganin cewa, ita ce xaya daga cikin hanyoyin da gardawa kan bi domin bayar da taimako. To, haka ma yin bitar wannan littafi, an yi ta ne domin a fahinci fasalin yadda gardawa kan koyi tsibbu, da kuma hanyoyin da suke bi su bayar da magungunansu. Ibrahim, M.S.(1982), ya kawo bayanai na yadda rayuwar Hausawa take kafin zuwan addinin musulunci da kuma bayan zuwansa.A lokacin da musulunci bai zo qasar Hausa ba, marubucin ya bayyana yadda27

addinin gargajiya yake na Hausa da kuma yadda Hausawa ke gudanar da shi. Haka ma a lokacin da musulunci ya zo qasar Hausa, marubucin ya bayyana maamar addinin musulunci da yadda ya yaxu a qasar Hausa da sauran qasashen Afirka. Daga nan kuma, sai marubucin ya ci gaba da kawo bayanai a kan muhimman abubuwan da musulunci ke koyarwa. Daga qarshe , sai ya kawo bayanai na yadda rayuwar Hausawa take a da, kafin zuwan musulunci da kuma a yanzu, bayan da musulunci ya zo.An yi bitar wannan aiki, domin marubucin, a cikin bayaninsa na zuwan musulunci qasar Hausa, ya xan kawo taqaitaccen bayani a kan sanaar gardancin karatu, a inda ya kawo bayani a kan matakai guda biyar kawai (watau kotso da titiviri da gardi da gangaram da kuma gwani) waxanda almajiri kan hau a wajen neman ilimin addinin msulunci. Bambanci aikin wannan marubuci da wannan aiki na sanaar gardanci shi ne, shi dai wannan marubuci bayani ya yi, kuma a taqaice, a kan gardancin karatu. Bai kawo wani bayani ba a kan sauran sanaoin gardanci na dabbobi ba da na wando da kuma na a-daki buzu. Haka kuma, ko a bayanansa na matakan da xalibi ke hawa a wajen neman ilimin addinin musulunci, marubucin ya kawo matakai biyar kawai, a maimakon guda tara. Madauci, I. Da Wasu (1968), sun kawo bayanai a kan yan hoto (ko yan dabo ko yan nakiya da garma), waxanda aladun da suke gudanarwa a lokacin bukukuwansu na shekara ya yi kama da na yadda gardawa (na wando) ke gudanarwa, a lokacin zagayensu na rangadi na28

shekara. Marubutan, a cikin bayanansu, sun kawo siffar yadda yan hoto suke, na barin tukkaye a kawunansu, da kuma irin walkin da suke xaurawa, da kuma irin dagumman(guraye da layu) da suke xaurawa. Waxannan duk siffofi ne da suka yi kama da na gardawan wando. An yi bitar wannan littafi, domin manazarta wannan kundi su qara gasganta da fahintar cewa, yawancin aladun da gardawa suke nunawa, a filin wasa, sun samosu ko sun taho da abinsu ne daga gargajiya, wanda suke gwama shi da musulunci.Haka ma Ibrahim(1982:89) ya gaskanta wannan qauli na cewa tazarce ne Hausawa suka yi wa aladunsu na gargajiya ya zuwa na Musulunci. Kuma an yi bitar wannan littafi domin manazarta su fahinci cewa, sanaar gardanci tana da alaqa da sauran sanaoin Hausawa na gargajiya,kamar sanaar noma. Haka kuna, bitar wannan littafi, za ta qara fito da sifofin da zaa iya gani a gane gardi, kamar ajiye tukku/tukkaye a kai, da irin sihirce-sihircensu. Musa, M.R.(1986), ya kawo zancen tashe, wanda ya ce almajirai ne kan kan yi, don tayar da mutane a lokacin sahur, na azumin watan ramalana. Haka kuma ya kawo bayanin a kan wasan tashe na ka yi rawa. A cikin bayaninsa, ya ce almajirai ne ke gudanar da wasan ka yi rawa, domin su nuna wa mutane qimar malamai da kuma sanaar malanta. An yi bitar wannan maqala domin a fahinci ta yadda almajirai kan koyi wasu wasanni na gardanci, tun suna a matsayinsu na xalibai.

29

Wannan zai sanya a qara gaskanta cewa, daga almajiranci ne gardi kan koyi sanaar gardanci. Nasarawa, S.H. (1997), ya kawo bayanai a kan maana, da tarihin gardanci, da irin mutanen da ake kira gardawa, da ire-iren gardawa, da kuma amfani da muhimmancin gardanci a aladance. Hakazallika, marubucin ya kawo bayanai a kan siffofin gardawan wando, da kayan aikinsu, da ire-iren macizan da gardawan macizai ke yin wasa da su, da yadda suka aiwatar da wasa, da wuraren da suke yin wasanninsu na gardanci, da kuma tasirin zamani a kan sanaar gardanci. Marubucin ya yi aikinsa a kan gardancin dabbobi da na wando kawai. Ko a bayanansa na gardancin dabbobi, ya faxaxa bayaninsa ne kan ire-iren macizai

kawai, amma kuma bai kawo hotunansu na zahiri ba, sai zane-zane kawai . Haka kuma bai kawo cikakkeun bayanai ba a kan gardancin kura da na biri da na kunama da kuma na karatu, sannan bai ce uffan ba a kan gardancin a-daki-buzu ba. Ken an, wannan bincike a kan gardanci bai zama cikakke ba. Sarari,S.U.M. (1989), ya bayyana maanar karin harshe da karin harshen matsayi. Haka kuma marubucin ya kawo bayani a kan sanaa, da dangantaka, da maaunan zamantakewa, da kuma ire-iren zantukan gardawa a matsayin malamai, da kuma mahauta. A cikin bayanan da aka yi na hira da malamai, an kawo salale (salo-salo daban-daban) na karatun gardawa da kuma irin taimakon da sukan bayar (watau magunguna) na30

rashin lafiyoyi daban-daban, waxanda suka sa malamai zama kamar likitocin alummar Hausawa. Bitar wannan kundi za ta qara sanya gaskanta cewa, lallai gardawa suna da irin salonsu na magana da suke yin amfani da shi. Haka kuma an yi bitar ne domin fito da muhimmancin gardawa ga alummar Hausawa, ba ma kamar ta wajen bayar da magunguna.Shi ma wannan marubuci bayansasun tsaya ne kan gardawan karatu kawai.Bai kawo komai ba akan sauran gardawan da qasar Hausa. Umar, M.B.(1980), na xaya daga cikin marubutan da suka bayar da gudummuwarsu a kan ayyukan da suka danganci almajiranci da malanta. Gardi kuwa, ba ma kamar na karatu, almajiri ne, kuma malami. Umar ya yi bayani a kan tashen ka yi rawa, wanda almajirai ne kan gudanar da shi, ta hanyar fito da siffofin malamansu, da kuma nuna irin qimar da malamai suke da ita a alummar Hausawa. Bitar wannan aiki zai sauqaqa fahimtar bayanin yadda gardawan karatu kan yi tazarce, daga bara, ya zuwa manyan makaxan Hausa, kamar yadda mutane irin su Alhaji Mamman Shata, da Muhammadu, Sarkin Taushin Sarkin Katsina, da dai makamantansu suka yi. Hausawa na cewa: Shagalin duniya, mai sanya malami da allonsa, ya haye ya bar buzunsa. Wani mawaqi mai suna Bala Mila, a wata waqa mai suna Dadin Duniya, yana cewa : Daxin duniya yakan riqa ruxin samari, Daxin duniya mai mayar da musulmai kafirai, Muna da imani, muna da addini.

31

Ke nan, shagalin duniya na iya sanya almajiri ya shiga ayyuka na sharholiyar duniya, kamar su kixa da waqa da dai makamantansu. Saboda haka, idan aka yi wa waxannan ayyuka, da aka yi bita, kallon idon basira, za a ga cewa, kowanne marubuci ya yi aikinsa ne a kan wani xan vangare daga cikin sanaar gardanci. Alal misali, Abubakar (2002), ya yi bayani ne a kan irin (salon) Hausar da gardawan karatu (na allo) ke amfani da ita a wajen maganarsu ta yau da kullum. Shi kuwa Alhassan (1982), ya yi bayanai akan gardawan karatu (na allo), da kuma ire-iren sihirce-sihircen da gardawan wando (watau yan dabo), ke yi a wajen gudanar da sanaarsu ta sayar da magunguna. Ango(2000) ma ya kawo bayanai ne akan gardawan karatun allo kawai. A cikin bayaninsa ma, bai fayyace dukkan matakan karatu da gardi kan bi ba, kafin ya kai ga matakin gardi, da kuma matakai na gaba da gardi. Bunza(1999), ya yi bayanai ne akan ire-iren siddabarun da masu wasa a dandali kan yi, da kuma yin amfani da xankore,a lokacin da suke yin tallar magungunansu, kamar yadda gardawan wando da na dabbobi (irin su kura, da biri, da macizai), kan yi. Bunza (2004), kuwa, bayani ya yi akan sanaar tsibbu, wadda sanaa ce ta gardawan karatun allo. Xangambo (1984) kuwa, bayani ya yi akan sanaar gardancin a-daki-buzu. Shi kuwa Garba (1991), bin sahun su Ango ya yi, domin bayani ya yi a kan sanaar tsibbu, wadda sanaa ce ta gardancin karatu. Madauci (1968) ma, bayanai ya kawo akan yan hoto, masu gudanar da wasanninsu kamar yadda gardawan wando32

kan gudanar.Amman kuma, ya zo daga baya ya kawo bayanai akan gardawan karatu. Musa (1986) ma, bayaninsa ya karkata ne akan gardawan karatun allo. Amma Nasarawa(1997), ya xan tavo bayani akan gardawan karatu da kuma gardawan wando,sai dai bai ce komai ba akan sauran gardawan qasar Hausa. Sarari (1989), kamar Abubakar ya ke, domin bayani ya yi akan salon Hausar da gardawan karatu kan yi

magana da ita. Umar (1980) ma, bayaninsa, ya yi shi ne akan gardawan karatu. Tiqashi ! Babu marubucin da ya yi bayani wanda ya haxe dukkannin sanaar gardancin qasar Hausa a cikin littafi ko kundi xaya.

1.2

BINCIKE. HUJJAR CI GABA DA BINCIKE. Sanaar gardanci sanaa ce da ta haxa musulunci da gargajiya,

wadda Hausawa suka daxe suna aiwatar da ita a qasar Hausa. Mutane da yawa sun yi aiki ko bincike a kan wanna tsohuwar sanaa, to, amman akwai wasu alamurra waxanda suka sanya ya zama wajibi a sake yin wani aiki ko bincike a kan wannan sanaa, ta gardanci a qasar Hausa. Domin a sake kallonta jiya da yau, kamar haka : Da farko dai, dukkanin waxanda suka yi aiki ko bincike a kan sanaar gardanci, sun yi ne a kan fanni xaya ko biyu kawai na sanaar, a maimakon dukkan fannoni na sanaar gardancin Hausawa. Abin nufi a nan shi ne, dukkan ayyukan an yi su ne a warwatse, wanda kowanne ya xauki vangare xaya ko biyu kawai, ya yi aiki a kansa, a maiamakon a yi33

aikin guda xaya, a cikin littafi ko kundi xaya a kan dukkaninsu. Ke nan, kusan dukkan ayyukan da suka gabata, ba su nuna alaqar dangantaka ba, a tsakanin sanaoin gardanci. Wannan wani cikas ne, a ganina. Saboda haka, ina ganin ci gaba da wannan aiki ko bincike ya zama wajibi, domin a kawo dangantaka a tsakanin sanaoin gardanci na jiya da na yau, ta hanyar haxa su a wuri xaya, a matsayin sanaa mai suna guda. Haka kuma, kusan duk waxanda suka yi aiki (ko bincike), a kan sanaar gardanci, sun yi shi ne a taqaice. Wasu kuwa, sun faxaxa bincikensu a wani vangare kawai na sanaar gardanci, amma suka taqaita wasu vangarori. Alal misali, Alhassan (1982), ya yi bayani ne a kan sanaar malanta da kuma dabon gardawa (na wando), sannan kuma ya taqaita bayanai a kan sanaar malanta da kuma dabon gardawa (na wando). Shi kuwa Xangambo(1984), a kan gardancin a-daki-buzu kawai ya yi bayani, kuma ma a taqaice ya yi bayanansa. Nasarawa (1997) kuwa, ya yi bayani a kan rukunnai huxu na gardanci, watau gardancin katatu, da na dabbobi, da na wando da kuma na gardancin macizai. A hakan ma, sai ya taqaita bayanan gardawan karatu da na dabbobi da na wando, amma ya faxaxa na gardancin macizai. Duk da haka, bai ce uffan ba ga sanaar gardancin a-daki-buzu. Su kuwa su Ango(2000) da Barkun (1990) da Abubakar (2002) da Sarari (1989) da Madauci (1968) da Bunza (2004), duk sun yi bayanai a kan gardawan karatu (na allo) ne kawai. Ba su tavo na gardancin wando ba ko na dabbobi, balle na gardancin a-daki-buzu.34

Wannan ai kamar yin tuya ne a manta da albasa. Bayani a kan gardanci, ba abu ba ne da za a yi a taqaice, ko a yi na wani vangare, a watsar da wani. Saboda haka, ya kamata a sami wani bincike wanda, baya ga haxe duk wasu fannoni na sanaar gardanci na qasar Hausa, ya kuma yi bayani yadda ake gudanar da kowacce sanaar gardanci,jiya da yau, a kammale, ba a taqaice ba, domin mutane su fahinci yadda kowacce take. Bugu da qari, duk kusan wani aiki da aka yi akan almajirai, ko malanta, ko neman ilimin addinin musulunci, babu wanda ya nuna, ko fayyace matakan da almajiri kan bi ko hau, dalla-dalla, na karatu, a makarantar allo (watau wajen neman ilimi), tun daga qolo/kotso har ya zuwa gangaram. Wannan ya zama baya ba zane, domin matakan nan na karatun allo, muhimmai ne ga harkar almajiranci ko malanta. Matakan ne ke nuna iyakar inda masu yin sanaar gardanci sukan kai, ga neman ilimi, kafin su zama gardawa. Haka kuma, sune kan nuna inda sanaar tsibbu ta fara, domin Mallam Ahibba ya ce, gardi ya fi kowa neman naqalin da ke cikin Alqurani, daga wajen malamai.7 Haka ma Alhassan (1982:69) da Garba (1991:106), duk sun yi bayanin cewa daga almajiranci ne akan fara koyon sanaar gardanci (watau tsibbu). To, tunda matakan nan suna da muhummanci ga sanaar gardanci, saboda haka, ya zama wajibi a sami wani bincike wanda zai fid do da matakan karatu na almajirci, wanda

7

Hirar Da Aka Yi Da Mallam[ Alaramma] Muhammadu Auwal Ahibba [Babarbare], Makarantar Allo Ta Ahibba, Bayan Asibitin Daji, Rijiyar Xorawa, Sakkwato.

35

masu neman ilimin addinin musulunci ke hawa kafin su zama gardi, da kuma gaba da matakin gardi. Daga qarshe, zamani da zamananci sai qara shigowa yake yi cikin qasar Hausa, ba ma kamar shigowar ilmin boko, da kuma wayewar kai, ta hanyar faxaxar da ilimin addinin musulunci ke samu, yau da kullum, waxannan na kawo barazana ga aladun Bahaushe, ba ma kamar waxanda suke da surki da maguzanci ko gargajiya. Faxaxar ilimin nan, ta sanya ko cusa wata qyama ga wasu sanaoin Hausawa na gargajiya, waxanda akan yi sihiri ko siddabaru da dabo, a wajen aiwatar da su.8 To, da yake, sanaar gardanci, sanaa ce da akan yi amfani da dabo ko sihiri, domin a sami kasuwar sayar da magungunan gargajiya, sai ya zamanto, wasu mutane da yawa, ba ma kamar waxanda ke zaune a birane, suna qyamatar masu gudanar da sanaarsu ta hanyar yin amfani da sihiri ko wata shiga mai nuna siffar mata ko xan daudu. Ganin haka, sai wasu masu yin irin wannan sanaa, suka shiga barinta. Wannan haxari ne ga nazari na aladun duniya, da kuma aladar Bahaushe. Yanzu haka sanaar gardancin a-daki-buzu da ta gardancin wando, sun vace a cikin birane, sai dai a qauyuka. Saboda haka, yin wannan bincike ya zama wajibi, domin a sami wani kundi, wanda zai zama kamar wata taska, ta ajiyar tarihin wannan sanaa ta gardanci a qasar Hausa, jiya da yau, domin a ajiye tarihin wannan sanaa, saboda barinta da masu yinta ke yi, domin alumma mai8

Hirar Da Aka Yi Da Mallam Shehu Ibrahim A-sha-dawo, Sarkin Gardin Dange, Sakkwato.

36

zuwa nan gaba, waxanda qila ba za su ci karo da masu yin sanaar ba, su duba su sami bayanin tarihin yadda ake gudanar da wannan sanaa. Baya ga Hausawa, Turawa ma masu yin bincike na iya bincika wannan aiki, wanda ya zama kamar ajiyar tarihi, domin su sami gaskiyar yadda ake gudanar da sanaar gardanci a qasar Hausa, a maimakon irin rubucerubucen qarya da sukan rubuta, na game da aladun yan Afirika.

1.3

BINCIKE. MANUFAR BINCIKE Bincike a kan sanaar gardanci a qasar Hausa, babban bincike ne

na tarihi, a kan tsohuwar sanaar Hausawa mai daxaxxen tarihi a qasar Hausa. Saboda haka, manufar da ta sa gudanar da wannan bincike tana da yawa kamar haka: Da farko dai, manufar wannan bincike ita ce ta samar da wani kundi na bincike, wanda ya haxa dukkan nauoi na ire-iren sanaar gardancin Hausawa na jiya da na yau, a wuri xaya, saboda alaqarsu da juna da kuma suna da suke da shi iri xaya. Bitar da aka yi akan ayyukan da suka danganci sanaar gardanci ya nuna cewar, babu wani kundi da ya tava haxe dukkansu a waje xaya, da sunan sanaar gardanci. Marubuta sun yi ayyukansu ne a kan fanni xaya ko fannoni biyu kawai na sanaar, a maimakon dunqule su a waje guda. Manufa ta biyu, ita ce ta neman wayar da kan mutane, musamman mazauna birane, masu qyamar gardawa (ta hanyar korar su, da gaya masu37

baqaqen maganganu in sun zo gidajensu yin wasa), domin yin shigar mata da wasu kan yi, (duba rataye na talatin da bakwai, a ga irin shigar da gardawan wando kan yi), ko sihirin da wasu suke yi, cewar sanaar gardanci, sanaa ce mai qima. Sanaa ce wadda ke xaya daga cikin sanaoi masu bayar da magungunan gargajiya ga alumma. Saboda qimarsu da muhimmancinsu,ya sa, a yanzu, a wannan zamani, ake neman taimakonsu a asibitocinmu, har akan xauke su aiki, domin irin gudummuwar da suke bayarwa ga fitar da rashin lafiyar da takan faskari likitocin zamani, kamar irin ciwon iskoki ko wanda ya danganci sihiri. Bugu da qari, wata manufar ta gudanar da wannan bincike ita ce ta samar da wani kundi, wanda zai zama wata taska, wadda za ta ajiye tarihin xaya daga cikin muhimman sanaoin Hausawa, kuma babbar aladar Hausawa ta gargajiya. Mallam Garba Nakande Azare, ya ce, yanzu zamani ya zo, wanda yayan gardawa ba su son su yi gadon sanaar iyayensu ta gargajiya.9 Ke nan, wata rana, za a wayi gari a iske babu sanaar gardanci, babu xuriyarta a qasar Hausa. Alal misali, yanzu ko xuriyar gardawan a-daki-buzu ba a ji. Gardawan wando ma, sanaar ta kusa vacewa, domin a qauyuka kawai ake gudanar da sanaar, ba a birane ba, domin, kamar yadda aka yi bayani a baya, qyamarsu suke yi a birane. Su kuwa masu sanaar gardin dabbobi,irin su kura,da maciji, ana yi masu kallon hadarin kaji, don ana ganinsu kamar irin mutanen nan masu yin9

Hirar Da Aka Yi Mallam Garba Nakande Matsango, Sarkin Gardin Sarkin Katagum, Azare, Jihar Bauci

38

fashi. Wannan ya sanya gardawa tsoron yin wasanni a kai a kai, don vata gari sun riga sun yava masu kashin kaji. Saboda haka, wannan bincike zai zama kamar wani kundi, wanda za a ajiye tarihin sanaar gardanci, domin alumma mai zuwa nan gaba, su tashi, su gani, su karanta, su amfana, su kuma san irin aladun iyayensu ko kuma kakanninsu da suka wuce. Haka kuma, kamar yadda na ambata a sama cewa, yanzu, a wannan zamani, vata-gari sun yi yawa, wato kusan kome ake yi na qwarai ko nagari, sai an sami wasu vata gari a cikin wannan abin. Akwai wasu masu sanaar gardanci, waxanda kan yi amfani da sanaar suna cutar da jamaar da ba su ji ba ba su gani ba.Alal misali, wasu gardawa, kan yi amfani da biri ko kura ko maciji, domin yin fashi da sata. Mallam Lawal mai kura ya labarta cewa, an tava kama irin waxannan vata-gari, a can wajen garin Tsamiyar-Giya, da ke kan hanyar zuwa Kano da kuma a can wajen qwanar Fara-qwai, da ke kan hanyar zuwa Kaduna.10 Wannan ya kawo vacin suna ga sanaar gardancii, ba ma kamar ta dabbobi. Saboda haka, xaya daga cikin manufar wannan bincike ita ce, fayyace wa jamaa da kuma hukuma ko gwamnati, ire-iren gardawan, waxanda suke yan asali, waxanda suka yi gado, masu bi gida-gida ko unguwa-unguwa, wajen gudanar da sanaarsu, da kuma vata-gari (watau jabu), waxanda yawancinsu yan haye ne, masu gudanar da sanaarsu ta gardanci a10

Hirar Da Aka Yi Da Mallam Lawal Mai Kura, Baki Kamfawul Qofar Gardi, Malumfashi.

39

kasuwa, tare da yankore. Ke nan, abin nufi a nan, shi ne, wannan bincike, zai fito wa da gwamnati irin gardawan da ya kamata ta riqa hana su wasanni, da kuma waxanda ya kamata ta bari. Domin a yanzu, hukuma takan hana gardawan dabbobi yin wasannin sanaarsu ta gardanci, ko kuma su kama su, idan an ji labarin cewa, an yi fashi a wani wuri, ta yin amfani da wata dabba muguwa. Wata manufar kuma ita ce ta fito da qimar wannan sanaa ta gardanci, domin wasu masu saurin zartar da hukunci na kai duka ko mari ko zagi, bisa ga abin da ba su da ilimi a kansa. Kalmar gardi da sanaar gardanci abubuwa ne masu qima da daraja a qasashen Hausa na Kano da Katsina da Zazzau da Bauci da Zamfafa, kai har ma a qasar da ba ta Hausa ba, irin su Barno, domin alaqar da kalmar da sanaar gardancin suke da shi da karatu ko neman ilmin addinin musulunci. To, amman a wasu qasashe, irin su Sakkwato da Kabi da Nijar, ana alaqanta sunan da sanaar gardanci a matsayin baqin suna da baqar sanaa, wadda masu yin ta ake kallonsu kamar maza-mata, masu yin shiga irin ta yan daudu. Salisu Audi Mabera, ya ce in aka kira mutum ko malami da sunan gardi a shiyyar Sakkwato da Kabi da Nijar, to, lallai sai an kai wa wanda ya kira mutum xin, mari ko duka ko a yi masa zagin da ba zai tava jin daxinsa ba.11

Salisu ya ci gaba da bayanin cewa, gardi a waxannan

shiyyoyi, na nufin mutum mara daraja, wanda ya wulaqantar da kansa ta11

Hirar Da Aka Yi Da Mallam Salisu Audi Mabera, Mai Kula Da Xakin Karatu Na Maaikatar Gona Da Gandun Daji, Sakkwato.

40

hanyar yin shiga irin ta mata, ga tukkaye (tsoraye) a kansa, sannan yana yin rawa da waqa da kixa, yana kuma yin sihiri. Ke nan, wannan bincike kamar wata ilimantarwa ce ga jamaa cewa, gardi suna da nauoi. Baya kawai gardin wando, wanda ke aiwatar da sanaarsu a qasashen Sakkwato da Kabi da kuma Nijar ne gardi ba, akwai wasu daban da ke amsa sunan gardi, to, amman malamai ne, akwai kuma masu wasa da dabbobi da wasu qwari miyagu. Daga qarshe, wata manufar da ta sa yin wannan bincike ita ce, ta takalo rina daga kaba. Abin nufi a nan shi ne, duk da cewa wannan bincike an so a zurfafa shi, to, amman ta yiwu, akwai wani fannin da ba a tava ba. Ilimin duniya yawa ke gare shi. Saboda haka wasu manazarta na iya leqo wani fannin da ba a tava ba, a kan sanaar gardanci, domin su ma su ce wani abu a ciki. Saboda haka,wannan bincike zai kasance kamar wata masoma ko wani masomi(mafari), na fara yin wani binciken a kan sanaar gardanci a qasar Hausa ko kuma a wasu qasashen da ba na Hausa ba, kamar Barno, domin sanaar gardi fage ne kandami a sha, a yi wanka, wato, fage ne na aladar Hausawa mai faxin gaske, wanda qure shi sai an yi da gaske, wai an ce dukan sauro da gatari.

1.4

HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE. Hanyoyin guda shida ne kawai aka bi domin gudanar da wannan

bincike na sanaar gardanci a qasar Hausa. Hanyoyin kuwa sun haxa da:41

Na farko dai, ni kaina mai yin binciken, na tashi cikin alummar Hausawa, na tarar da, aqalla, jinsi shida, na gardawa, masu yin sanaar gardanci. Hasali ma garinmu, Malumfashi, kusan shi ne dandalin gardawa. Haka kuma, saboda harkar gardanci ne ya sanya maigirma Galadiman Katsina, watau hakimin Malumfashi, ya ba sarkin gardin sarkin Katsina, unguwa guda, domin ya kafa fadarsa ta gardawan dabbobi. Har ila yau, akwai kuma gardawa na karatu a Malumfashi, waxanda ke yin karatun allo, kuma suna da alarammominsu masu tuammali da harkar karatun Alqurani. Baya ga haka ma, kusancin da Malumfashi take da shi da Kano, ya sanya ba a yin wata, ba tare da wani Shehun Malami, baqo, ya kawo ziyarar rangadi zuwa Malumfashi ba. Wannan ya sanya, kusan duk lokacin kaka, na kowacce shekara, sai an gudanar da bukukuwa iri-iri na gargajiya, irin su kalankuwa da bikin shan kara-rake da bikin wasan wuta na maqera da bikin rawar bugaje da wasannin yan dabo da yan tauri da ake gudanarwa, a ranar cin kasuwar garin (jumaa da talata) da kuma waazin fitilar ruwa, wanda gardawa ke gudanarwa a unguwanni, da daddare, da dai sauran harkokin alada da addini. Saboda haka, ilimin da na tashi da shi, a sanadiyyar tashi a cikin gardawa, ya qarfafa qwarai a wajen rubuta wannan bincike. Haka kuma, hanya ta biyu, ita ce, wadda, a lokacin da gardawa suke yin wasanninsu, sai nakan shiga cikin yan kallo, ina kallon yadda suke yin wasanninsu, kuma da yadda suke bayar da taimakonsu na tallar42

magunguna irir-iri, na rashin lafiyoyi daban-daban. A nan, ina yin kallo, ina kuma rubuta abubuwan da na gani, ba tare da gardawan sun san irin abin da nake yi ba (duba rataye na ashirin da tara da na talatin da xaya da kuma na talatin da biyar, a ga yadda mai bincike ke kallon wasan gardancin wando). Hanya ta uku, ita ce ta gabatar da kaina, gaba-da-gaba. A nan, na kan kai ziyara, wurin gardawa, a lokacin da suke wasanninsu na shekara, na kan kuma faxa masu manufar ziyara ta, watau yin bincike a kan sanaarsu, sukan kuma yi naam, su ci gaba da yin wasanninsu, ni kuma ina kallo, ina kuma yi masu yi masu tambayoyi, suna amsa mani, ina rubuta amsar da suka bayar a cikin littafi (duba rataye na 28 a ga yadda mai bincike ke yin tambayoyi ga gardawa). Bugu da qari, baya ga rubutawa da nake yi na amsoshin da gardawa suka ba ni, nakan kuma tafi wuraren da gardawa ke yin sanaarsu tare da naura mai xaukar sauti ko magana (watau rikoda), da naura mai xaukar hoto (watau kyamara), da kuma naura mai xaukar majigi (watau hoto da magana da motsi, mai suna bidiyo), domin xaukar waqoqi da raye-raye da sauran maganganu na amsoshin tambayoyin da nakan yi wa gardawan(a duba rataye naashirin da takwas a ga yadda mai bincike ke amfani da rikoda). Wata babbar hanyar da na gudanar da wannan bincike ita ce wadda na sadu da sarakunan sanaar gardanci, a gidajensu,(ba a dandalin wasa43

ba), na kuma yi masu tambayoyi, suka kuma amsa mani, na kuma rubuta. Idan akwai wanda ya kamata a sanya a cikin naurar majigi ko wanda ake so a xauki hotonsa, duk na yi (duba rataye na ashirin da takwas, a ga rikodar da mai bincike ya yi amfani da ita a wajen yin bincikensa). Hanya ta biyar, ita ce ta sauraren gidan rediyo na Kaduna, watau sauraren Filin Halittu Gida Da Na Daji, wanda Mallam Sani Muhammed Qanqara, kan gabatar. A cikin wannan filin ne akan faxi tarihin dabbobi iri-iri, kuma akan yi hira da gardawan dabbobi dabandaban. A haka ne na kan sami wasu bayanai na wasu halittun da gardawa suke yin wasa da su, kamar irin su kura, da biri, da kuma macizai. Daga qarshe, hanya da ta taimaka wajen gudanar da wannan bincike, ita ce ta karanta wasu littatafai, waxanda wasu bugaggun littattafai ne, wasu kuwa kundaye ne na neman digiri, wasu kuma qasidu ne, da mujallu da kuma jaridu. Wasu na mallake su tun ina xalibi, wasu kuwa sayensu na yi a lokacin da nake yin wannan bincike, wasu kuwa malamai na, irin su Shaihun Malami Bunza. A. M., da Mallam Habibu Sani Vavura, na Jamiar Bayero, ta Kano, da Mallam Ibrahim Malumfashi, na Jamiar Usumanu Xanfodiyo, Sakkwato, suka ba ni kyauta. Wasu kuma a xakunan karatu na zauna na karanta. Ke nan, wannan bincike, ba abu ba ne na yau ko yanzu ba, abu ne wanda na tashi a cikinsa, na yi cuxanya da shi tun ina xan yaro, har ya zuwa girma na da kuma ilimi na na almajiranci na karatun allo da kuma44

rayuwata ta yawon neman ilimin boko da yin aikin koyarwa a qasashen Barno da Bauci da Kano da Zazzau da Katsina da kuma Sakkwato. 1.5 KAYAN DA AKA YI AMFANI DA SU WAJEN YIN BINCIKE. Wannan bincike na sanaar gardanci a qasar Hausa, bincike ne da ke buqatar shiga cikin fagen da ake gudanar da sanaar. Saboda haka, kayan da aka yi amfani da su, domin gudanar da binciken, duk kaya ne da ake iya shiga cikin fage ko dandali ko filin wasa da su, don tatsar bayanai. Da farko, an yi amfani da rikoda, watau naura mai xaukar sauti ko magana, domin xaukar duk bayanai, da amsoshin tambayoyin da aka gabatar zuwa ga gardawa. Wannan naura tana da faifai (wato kaset), wanda yake naxar bayanai, saboda haka, an yi amfani da waxannan kaset-kaset, domin naxar bayanan da aka xauka. Haka kuma, an yi amfani da naurar xaukar hoto, domin xaukar hotunan Sarakunan gardawa da wakilansu da yaransu da kuma kayan da suke amfani da su, domin gudanar da sanaarsu. Ni mai bincike, ba ni ke xaukar hotunan da kai na ba, na xauko hayar wani mai xaukar hoto ne, mai suna Alhaji Muktar Xanbini, kuma yakan xaukar mani duk wanda na ce ya xauka. Bayan haka, an yi amfani da naurar majigi, domin xaukar irin wasannin da gardawa ke yi. A nan ma, ba mai binciken ba ne ka rungume da naurar, ya yi haya ne na wani mutum wanda yake bin mai binciken45

cikin birni da qauye, domin xaukar duk abin da aka ce ya xauka. Da yake wannan bincike ana son ya zame kamar taska na ajiyar tarihin sanaar gardanci a qasar Hausa, saboda haka, qwararren mai xaukar majigi ne aka xauko, domin yin wannan aiki, don gudun kada a sami wani babban kuskure. Daga qarshe, mai yin bincike ya yi amfani da babur (ko mashin), don gudanar da wannan bincike. Yin amfani da babur ya zama kusan wajibi, domin ya fi sauqin a yi amfani da shi domin shiga cikin qauyuka, a zaqulo gardawa, don yi masu tambayoyi. Yawancin gardawa, na karatu da na wando, an fi samunsu a qauyuka, saboda haka, babur ne kan iya isa zuwa gadajensu.

1.6

MATSALOLIN BINCIKE. BINCIKE Bincike irin wannan, wanda ya zamana dole mutum ya shiga

cikin duniya, ya yi tafiye-tafiye, ya kuma yi cuxanya da jamaar da yake son tatsar bayanai a gare su, bincike ne mai tattare da matsaloli masu ximbin yawa. Bugu da qari, dukkan mutum ajizi ne, domin tara yake bai cika goma ba, saboda haka, matsalolin da aka ci karo da su sun haxa da : Da farko, akwai matsala ta yin tafiye-tafiye, da zirga-zirgar zuwa unguwanni da qauyuka da kuma garuruwa irin su Kano da Bauci da Zazzau da Kaduna da Katsina da Kuma Barno, domin neman bayanai.46

Hausawa na cewa : Tafiya, wani yanki ne na azaba. To, abin haka yake, domin tafiya, ko da a cikin mota ne, ba ta da daxi, saboda daxewa da mutum kan yi, ta zama a cikin mota, ga gajiya, ga jin yinwa, ga fargabar haxari ko gamuwa da varayi, da kuma fargabar gudun lalacewar abin hawa a cikin daji. A irin haka ne, a loacin gudanar da binciken nan muka sami faci, a tayar baya ta babur (mashin) xin da muka hau, ni da mai xaukar hoto, zuwa qauyen Mujiya, da ke qarqasin Dabagin Ardo, a can qasar Shuni. Bayan mun kwana, mun yi kallon wasannin gardawa na dare, sai muka tashi da safe, don mu bi gardawan zuwa wani qauye, don mu qara ganin qwaf, to, amman sai facin ya hana mu. Ba a samun mai yin facin tayar babur a Mujiya, sai dole da muka zo Shuni. Ba na tava mantawa da ranar nan, domin mun sha wahalar turin babur, ga qishirwa, ga yinwa, ga kuma nauyin kayan xaukar hoto. Matsala ta biyu, ita ce matsalar kashe kuxi. Wannan bincike ne da yake buqatar kuxi masu yawan gaske. Baya ga kashe kuxi a wajen buga kundin bincike, haka ma mutum na kashe kuxi masu yawa wajen yin tafiye-tafiye, da xaukar hotuna, da sayen batiran naurorin xaukar hoto, da ta xaukar magana. Haka kuma mutum na kashe kuxi qwarai domin biyan waxanda ake samun bayanai wajensu. Wata matsalar kuma, wadda aka ci karo da ita, a lokacin gudanar da wannan bincike, ita ce ta rashin kuxi, a dalilin wata rashin lafiya da

47

matata ta samu. Wani mawaqi mai suna Musa Daudu, a cikin waqarsa mai suna Dan Gudubale, yana cewa : Ina ma ina ma, Ina ma da Naira, In more arziqina, Allah Ka aiko da Naira, In more arziqina. Wannan rashin kuxi ya sanya na tari aradu da ka, na yi amfani da ilimin naura mai qwaqwalwa, watau kwamfita, da wata sabuwar shugaba da muka yi a wajen aikin mu, mai suna Mrs Ijasan, B.O., ta sa aka koya mana, don buga wannan aiki. To, abinka da xan koyo, sai da na kai qarshen aikin, ina ta tattalin in faifaye, in kai wa jagorar wannan aiki, sai kawai na danna wani abu, aikin ya vace. Kusan babu wanda ban kira ba domin ya cetar mani wannan babbar wahala da na yi, saboda rashin kuxi, amma abin ya ci tura. Dole sai da na faro buga aikin daga farko. Haihuwa xaya horon gindi. Hausawa na cewa: Ana dara, ga dare ya yi. Abin nufi shi ne, ga shi jagorar aikin nan na son in kawo domin ya duba, domin yanma son zai tafi Misira, ga shi kuma aiki ya vace a cikin naura mai qwaqwalwa (kwanfuta). Har ila yau, bayan an kamala aiki, an kai wa jagorori su duba, bayan sun duba, sun bayar da gyare-gyaren da zaa yi, sai aka sake san ya aikin a cikin naura mai qwaqwalwa. Ana cikin yin gyare-gyaren, sai da aka kusa gamawa, sai naurar ta sake lalacewa. Kai Sai da dai na sayi wata naurar, mai kyau, sannan na sami damar gama aikin.48

Wata kuma babbar matsala da na samu ita ce ta lalacewar naura mai xaukar magana (watau rikoda), a lokacin da nake gudanar da wannan bincike. Yadda abin ya faru shi ne, bayan na yi saitin naurar, ashe akwai wani fanni, wanda na danna, sai kawai naurar ta ta yi ta xaukar banza, ba magana. Sai bayan da na dawo gida, domin gwada abin da na xauka, na gane illar. Wannan ya sanya dole na sake shiga daji (qauyuka), domin sake maimaita xaukar bayanai. Kuma duk da haka, Allah Ya sa na kan tafi bincike tare da mai xaukar hoto da kuma majigi. Wannan ya sanya matsalar ta zama da sauki. Wata babbar matsalar da aka ci karo da ita a wajen gudanar da wannan bincike, ita ce ta wahalar tatsar bayanai daga mutanen da ba su yi ilimin boko ba. Hausawa na cewa: Abin da kamar wuya, wai gurguwa da aure nesa. Wani lokaci, sai mutanen su qi bayar da wasu bayanai, domin suna ganin kamar ana neman a san sirrinsu ne. Wani lokacin ma sukan kalli mai bincike, kamar wata hukuma, wadda ta zo ta nemi sanin abubuwan da suke aiwatarwa, domin a turo masu yansanda su kama su. A irin nan, hanyoyi biyu na bi domin warware wannan matsala. Na farko dai, nakan saki jiki na, in rinqa yi wa gardawa ladabi da biyayya, da cin abincin duk da suke ci, da kwana wurin da suke kwana, da kuma bin su sallah a cikin sahu. Wannan ya sanya aka saki jiki da ni, aka yi ta ba ni bayanai, ina tatsa, ina rubutawa, ina kuma xauka a cikun naurori. A wasu wurare, sai da na bi qaidar xaukar asiri na sanaoi kafin aka yarda aka49

ba ni baya nai. Alalmisali, a Sakwwato, sai da sarkin gardin sarkin Musulmi ya bayar da izini, kafin aka yarda aka ba nai bayanai.

1.7

NAXEWA. A cikin wannan babi na xaya, an gabatar da maanar sanaar

gardanci a ma tsayinda kuma shimfixar ta aikin . Haka kuma, an gabatar da bitar ayyukan da suka gabata, masu alaqa da sanaar gardanci, da hujjar ci gaba da wannan bincike, da manufar yin binciken, da kuma hanyoyin da aka bi aka yi wannan bincike.

50

BABI NA BIYU. 2.0. 2.0. SANAOIN TARIHIN SAMUWAR SANAOIN GARGAJIYA A ALAQARSU QASAR HAUSA DA ALAQARSU DA SANAAR GARDANCI. GARDANCI ANC Sanaar babbar alada ce mai muhimmancin gaske ga xan Adam. Mutumen da duk ya kama wata sanaa, tamkar ya shiga wani kungiya (Kulob) ne (Alhassan, 1982: 31), domin kowacce sanaar Hausawa ta gargajiya, tana da aladunta na daban, da ake aiwatar da ita. Hausawa na cewa babu maraya sai raggo. Ke nan, Hausawa mutane ne masu bayar da muhimmanci ga sanaoi da kuma duk wani mutumin da zai sami abin yi (watau sanaa), ya riqe kansa, don kar ya zama abin tausayi. Ita kanta sanaa, wata dabara ce da xan Adam ke yi, ta hanyar sarrafa albarkatun da Allah Ya haltta a kewaye da shi, domin ya biya buqatunsa na yau da kullum. Haka kuma, aiki ne sanaa, wanda mutum zai aikata, domin ya sami amfanin da zai fito da darajarsa da ingancinsa da martabarsa da kuma bajintarsa, a idon alummar da yake ciki (Yahaya,1992:48). Buqatun rayuwa na xan Adam, na yau da kullum, irin na abinci, da muhalli da sutura da tsaro da sauran makamantansu, ke sanya xan Adam ya qirqiri sarrafa albarkatun da Allah Ya yi masa (sanaa), irin su farauta da noma da qira da saqa da sassaqa da fawa da gini da sauran

51

irinsu, don ya biya buqatunnsa (Yahaya,1992:48 da Alhassa,1982:59), a matsayin sanaoi na gargajiya.

2.1. 2.1. ASALIN SAMUWAR SANAOIN GARGAJIYA NA HAUSA A QASAR HAUSA KAFIN ZUWAN MUSULUNCI. Sanaa a qasar Hausa, abu ce mai daxaxxen tarihi. Hausawa na cewa: Tun kafin a haifi uwar mai sabilu, balbela ke da farinta. Abin nufi shi ne, tun filazal aka ga Hausawa da sanaoinsu na gargajiya. Tun ran gini, ran zane. Ke nan, a tarihance, babu wani ko wata alumma da ta tasa Hausawa a gaba, don ta koya masu yadda ake yin sanaoi. Tun faruwar kafuwar zaman Hausawa a farfajiyar da ake kira qasar Hausa, suka tashi da iya sarrafa albarkatun da Allah Ya halitta a kewaye da su, suna biyan buqatunsu, na rayuwar (Ibrahim,1982:117) Wasu masana tarihin qasar Hausa da harshenta, irin su Bunza(2006) da Philps(1985) da Magaji(1985) da Smith(1983:21), suna ganin cewa, Bahaushe ya samo dabarun iya sarrafa albarkatun da Allah Ya ba shi, tun daga Misira, a lokacin da yake a can gefen kogin Maliya. Domin ana ganin cewa, Misira gari ne mai ximbin tarihi, wanda yake qunshe da aladu da addinai daban-daban. Haka kuma, ana gani garin Misira, a matsayin cibiya ta sanaoi iri-iri, inda jamaa, farare da baqaqe, sukan taru, su yi ta sarrafe-sarrafen albarkatun da Allah Ya yi masu na yau da kullum

52

qasa. To, tunda Hausawa, a tarihance, sun fito ko villo ne daga gefen kogin Maliya, wannan ya sa su koyon yadda za su yi sanaa, tun kafin su yiwo qaura zuwa matsuguninsu na yanzu (watau qasar Hausa). Bin diddigin asalin faruwar sanaoin Hausawa, a qasar Hausa, babbar aniya ce, jifar sauro da gatari. Abin nufi a nan shi ne, abu ne mai wuya, wai an ce, gurguwa da aure nesa. Kamar kowacce alumma ta duniya, haka ma Hausawa, sun fara yin sanaa ne domin neman biyan buqatun rayuwa (Yahaya,1992:48), na abinci. Abinci kuwa wajibi ne ga xan Adam, don haka, yin sanaa don biyan wannan buqata ya zama wajibi, ba mustahabbi ba (Alhassan,1982:59). Ke nan, dole ce, qanwar na qi, ta sanya Bahaushe ya yi amfani da hikimar da Allah Ya yi masa, ya qirqiri yadda zai sarrafa albarkatun da ke kewaye da shi. Sanaar farauta, ita ce babbar dabara ta farko da Bahaushe ya fara yi a lokacin da ya zo qasar Hausa (Alhassan,1982:45 da Dokaji,1958:5 da Galadanci,1992:32 da kuma Garba,1991:111). Farauta ita ce sanaar da ta dace da lokaci da yanayin da Hausawa suka zo qasar Hausa. A lokacin da suka zo, a tsaitsaye suka zo qasar Hausa, daga gefen kogin Maliya da kuma tafkin Cadi (Magaji,1985 da Philips,1985), suna yawo, suna neman wurare masu dazuzzukan da akan iya samun dabbobi da tsuntsaye. Rimmer (1948:37), ya tabbatar da cewa, a lokacin da Hausawa suke a bakin tafkin Cadi, suna samun abinci mai kyau, da dabbobi, da isasshen ruwa. Ke nan, tuni suka saba da yin tuammali da dabbobi, tun kafin su53

iso qasar Hausa. To, da suka iso, sai suka ci gaba da yin tuammalinsu da dabbobi, da tsuntsaye (watau farauta), suna kama su, don biyan buqatunsu na abinci. Sukan yi amfani da qarfi da kuma dabarun da Allah Ya ba su, don mallakar dabbobin. Saboda haka, farauta ita ce sanaar farko da Bahaushe ya fara, da ya zo qasar Hausa, domin tarihi ma ya nuna cewar Hausawan da suka fara zama a Kano, maharba ne (Dokaji,1985:5 da Idi,1982:1). Haka ma a Katsina da Kwatarkwashi, maharba ne suka fara zama a Durvi-ta-kusheyi (Adawa), da kuma gindin dutsen Kwatarkwashi (Usman, 1981:5-8). Ke nan, sana,ar gardancin dabbobi, irin su kura da biri da maciji, sanaa ce da Bahaushe ya saba da ita tun da ya zo qasar Hausa. Tun kafin zuwan musulunci qasar Hausa, maza su ne aka sani da yin farautar manyan namun daji da tsuntsaye, amma mata da qananan yara, su ne ake bari a masauki, domin kula da yaya da gyara abincin da aka farauto. Duk da haka, matan ba zaune kawai suke ba, su ma sukan yi farautar qananan namu, irin su qadangaru da veraye da fari (Rimmer, 1948:41). Ashe wannan shi ya sa babu mata gardawa, masu yin sanaar gardanci da manyan dabbobi, irin su kura da biri, sai dai kawai qanana, irin su kunami da qananan macizai. Aladar kirari, wata sanaa ce tsohuwa wadda Bahaushe ke yin ta tun da ya zo qasar Hausa, wadda kuma ake sa ran ya fara ta ne daga farauta. To, da yake farauta, ba mutum xaya ne ke zuwa yin ta ba (Garba,54

1991:112), jamaa ne da yawa ke taruwa a wuri xaya, bayan an yi gangami, sannan a fantsama zuwa daji, a tafi neman naman dajin da za a kama. A duk lokacin da wani daga cikin mutanen (mazajen), ya nuna wata babbar bajinta ko hikima ko dabara, a wajen kama wata dabba ko tsuntsun da ya gagara, sauran mutane kan yabe shi. Ta haka ne Hausawa suka sami iya cusa yabo da kirari, a duk lokacin da suka yi wani aiki na bajinta. Da sannu-sannu, sai kirari da yabo suka haifar da waqa. Yahaya (1992:22) ma, ya yarda da wannan qauli, da ya ce, waqa ta faru ne a sanadiyyar farauta. Ba ja, wai an ce kare ya mutu a saura. Ashe dai kirari da waqe-waqen da gardawa ke yi a lokacin da suke yin sanaarsu ta bajinta, sila ya samo, daga farauta.Wannan shi ya sa ake ganin kamar sanaar gardancin dabbobi daga farauta ya samo asali. Bugu da qari, wata sanaar da Hausawa suka tsiri yi a lokacin da suka zo qasar Hausa, kafin musulunci ya zo, ita ce sanaar qira. ita ma wannan sanaa, ana sa ran tana da alaqa sa sanaar gardanci. Hausawa, maqeran farko, da suka tsiri yin sanaar qira, a qasar Hausa, tarihi ya nuna cewa mafarauta ne, waxanda a garin yawon farauta, suka ci karo da duwatsu masu albarkar, tama(iron ore (Newman,1997:142), wanda ya haddasa zamansu a gindin duwatsun Dala da Gwauron Dutse da Magwan, da kuma Fanisau, da ke farfajiyar Kano (Dokaji, 1958 :5). Haka ma a Katsina, maharban da suka zauna a Durbi-ta-kusheyi, su ne suka zarce zuwa yi noma da qira (Usman,1981:7). A Kwatarkwashi ma, duk zancen55

xaya ne (Usman, 1981:7). Rimmer ( 1948 : 121-122), kuwa, bayyana yadda maqera kan sarrafa dutsen tama, har ya zama qarfe ya yi. Sarkin Taushin Sarkin Katsina, Alhaji Muhammadu, don ya qara tabbatar da cewa Hausawa suna yin amfani da tama, sai ya yi amfani da sunan tam, domin ya gwarzanta sarkin Zazzau, Aminu, a inda ya ce: Mamman tsakin tama, gagara tauna ba ja da kai wargi ba, Tsoronka akai, uban Zagi, hadarin safe mai ba uban wani, Kashi. Abin lura a nan shi ne, su maqera, gwanaye ne wajen yin wasan wuta, da sauran waibuwoyi irin ta Sarkin maqera da mutanensa (Yahaya,1992: 59). To, ashe daman waibuwoyin da gardawan wando kan nuna a dandali, tushe abin ya samo. Lallai! Gardi gar da gar ! Wato, komai gardi ke yi a wajen wasan sanaarsa, a fili yake yi, kowa na ganinsa quru-quru. Sanaar noma ma na da silalin faruwarta daga sanadiyyar yin farauta, kuma sanaar gardanci ta xan samo wasu abubuwa daga gare ta. Dokaji ( 1958:5), ya bayyana cewa: .da waxannan maharba suka jarraba xan noma suka ga wurin yana da albarka,sai suka ci gaba suna qara saran daji suna yin gonaki. Ke nan, a can Kano, baya ga farauta, Hausawan da suka fara zama a can, noma ne suka fara gwadawa. Wannan ta yiwu, tun can asali, a gefen kogin Maliya da tafkin Cadi, sukan ya shi (noma), kafin su zo qasar Hausa. Rimmer (1948:40-43), kuwa cewa ya yi, tun farkon faruwar xan Adam, a duniya, noma ya fara yi, to, amman da ya sava wa Ubangiji56

Allah, sai dabarar ta vace masa, ya shiga duniya, ya zama mafarauci. Ke nan, Bahaushe, ya iso qasar Hausa a matsayin mai yawon farauta. Sai bayan da ya natsu ne, a wuri xaya, sai ya fara gwada noma, har ya kai ga cin nasara, (Salihu,1985:1 da Rimmer,1948:41-43). Manoma, a cewar Madauci (1968: 73-77) da Yahaya(1992:59), sukan nuna waibuwoyi irin na sihiri iri-iri, a lokacin wasanninsu na nakiya-da-garma (ko yan hoto), waxanda suka yi kama da na waxanda gardawan wando kan nuna a lokacin sanaarsu ta gardanci. Ke nan, sanaar gardanci tana da alaqa da sanaar noma. Daman yawancin gardawa manoma ne, wanda shi ya sa sai da kaka sukan gudanar da sanaarsu, bayan an kawar da amfanin gona. Wata kuma babbar sanaa, wadda ta danganci rayuwar Bahaushe, a fannin neman waraka daga ciwo, ita ce ta bokanci. Ibrahim(1982:304) da Garba(1991:93) da Yar-tsakuwa(2000:21),sun bayyana cewa, bokanci sanaa ce wadda Hausawa ke yi, domin maganin ciwo na aljanu ko makarai. Haka kuma, bokanci hanya ce ta faxin yadda wani abu zai kasance, kafin ya faru (watau faxin gaibu). Bunza(2004:4) da Galadanci(1992:75) da Ibrahim(1982:88) da Sarkin Sudan (2000:78), sun bayyana cewar, kafin zuwan musulunci, tubalan da Bahaushe ke yin amfani da su, don gina magungunansa na gargajiya, sun haxa da tsirrai, da ita ce, da albarkatun qasa. To, amman sai Garba(1991:95), ya kawo irin abubuwan da boka ke yi, a matsayin sanaa, kamar su xamaru, da kambu, da kwalba mai xaurin karare da sillaye, da layu, da rigar layu, da57

rataye da sauran makamantansu. Ke nan, tun da ma can, kafin zuwan musulunci, Hausawa suna da hanyar da suke tuammali da tsirrai da aljanu, domin samar da magungunan gargajiya, wanda daman shi ne babban jigon abin da gardawa suke yin talla, wanda ta kai su da yin wasanni, don neman jawo hankalin jamaa bisa ga abin da suke talla (watau magungunan gargajiya).(A duba rataye na 17, a ga irin kayayyakin da boka ke amfani da su, a wajen sanaarsa ta bokanci). Haka kuma, wata sanaar mai dangantaka da bokanci, ita ce ta bori. Boka ba xan bori ba ne, to, amman yana da alaqa ta ququt da su, saboda yin harka da aljanu. Garba (1991:100), ya bayyana cewa, Hausawa, a da, sun xauka cewa aljanu yayan bokaye ne, masu kawo masu kuxi. Amma a cewar Bunza(2005:5), ba kowanne Bahaushe ne xan bori ba, amma duk wani bokan da ke bayar da magungunan iskoki, xan bori ne. Saboda haka, sanaar bori, sanaa ce da ake yi wa mutum girka, domin a zaunar da iskoki a kan dokinsu, domin su daina wahalar da shi, da kuma fitar da iskoki a kan dokinsu (mutum), idan sun ki aminta su zauna lafiya a kansa, da samar wa mutum izinin zama xan bori cikakke, mai cin gashin kansa, da kuma warkar da cutar da iskoki suka haddasa a kan dokin da suke qauna ko suke adawa da shi (Bunza,2005:7). Galadanci (1992 :74-75) da Ibrahim(1982:304) da Umar(1985:14), sun bayyana cewa, daga wajen yan bori ne Hausawa suka sami yawancin camfe-camfen da suke amfani da su, don tafiyar da rayuwarsu a da can,58

kafin zuwan musulunci. Su kuwa su Bichi(1991:1) da Yar tsakuwa (2000:75), kawo maanar camfi suka yi domin su taimaka a gane tushe sanaar gardanci a qasar Hausa. Sun ce, camfi yarda ce ko amincewa da wani abu, ko aiwatrwa, wadda asalinta daga jahilci ne ko duhun kai ko tsoro da nuna fargaba ga abin da ba a tantance da shi ba, ko amincewa da wani sihiri ko sanadi maras tushe ko samuwar wani abin da ba a san asalinsa ba. To, idan dai haka ne, ke nan, ba shakka gardawa, ba ma kamar na wando, suna da alaqa da ya bori, domin irin sihiri da camfecamfen da suke riqe da su, waxanda sukan bayar ga Hausawa masu amsar magungunansu na gargajiya, sun yi daidai da irin wanda yan bori suke bayarwa. Saboda haka, kafin musulunci ya shigo qasar Hausa, akwai sanaoin gargajiya barkatai, waxanda masu yin kowacce sanaa suke zaune a unguwa guda, inda suke gudanar da irin sanaarsu (Naniya,1978: 3). Waxannan rukunoni na unguwanni na masanaantu, ba haxe suke ba a wuri xaya, kamar yadda qasar Hausa baki xayanta ba a dunqule take ba, a waje xaya (Alhassan,1982:73 da Ibrahim,1982:3). Warwatse suke, amma kusa da juna. Unguwar makera ba haxe take da unguwar majema ba. Haka ma unguwar masaqa ba haxe take da unguwar mahauta ba, ko majema ko dai wata sanaa. Kowacce sanaa tana da nata matsuguni da ake aiwatar da ita. Bugu da qari, a kowacce unguwa akan sami wani mutum wanda ya fi kowa nuna bajinta ko qwarewa ko nuna wata dabara59

ta daban a cikin sanaar da ake yi. Wannan shi ne akan xauka da daraja sosai, kuma takan sa a ma naxa irinsu a matsayin shugaban wannan sanaa (Alhassan, 1982: 75). Irin waxannan ayyuka na bajinta, waxanda akan nuna a cikin sanaoin Hausawa na gargajiya ne wasu (gardawa), suka xauka, suna yi ko gwadawa domin su jawo hankalin jamaa zuwa ga sayen magungunan gargajiya da suke yi. Bari mu ga ire-iren waxannan hanyoyi na gwaninta da ke cikin wasu daga cikin sanaoin Hausawa na gargajiya, waxanda gardawa suke yin amfani da su, don gudanar da sanaarsu. 2.2 HANYOYIN NUNA GWANINTA A CIKIN MUSULUNCI. A wancan zamani, kafin musulunci ya shigo qasar Hausa, kowacce sanaar gargajiya ta Hausawa, wadda Bahaushe ke gudanarwa a unguwoyi, tana da wasu hanyoyi na fasaha, da hikima, da dabaru na nuna gwaninta da waibuwoyi a cikinta, da kuma dabaru na bayar da magunguna, don kiyaye lafiyar masu gudanar da ita (Yahaya,1992:59). Irin waxannan dabaru akan gwada su a lokacin gudanar da wasu bukukuwa na wannan sanaar, ko a lokacin samuwar wani abin farin ciki a gidan da ake gudanar da irin wannan sanaa, ko kuma a cikin unguwar ko garin da ake gudanar da wannan sanaar. Ana yin ko nuna waxannan dabaru na qwarewa domin neman qara wa sanaar da kuma masu yinta, SANAOIN

HAUSAWA NA GARGAJIYA KAFIN ZUWAN

60

qima da daraja, a idon mutane. Yawanci, akan yi amfani da aljanu ko rauhanai, domin samun ilimin aiwatar da yawancin siddabarori da walankeluwa da wasu dabaru na mamaki, a cikin sanaoin gargajiya na Hausa, kafin zuwan musulunci(Ibrahim,1982:36). Galadanci (1992: 32), ya ce: Kafin zuwan musulunci,Hausawa suna bautar iskoki ne da kuma tsafe-tsafe. Kowanne gari da tsafin da suke bauta wa, kamar su tsumburbura, gajimare, magiro, uwar dawa da sauransu. Haka ma Usman (1981:13-14), ya bayyana cewa, a Katsina, tun a farkon qarni na goma sha biyar, masu shugabantar sanaoi, su ne kuma ke shugabantar harkar bauta. Misalansu sun hada da, magajiyar bori,da uban farauta, da magajin rafi, da kuma Sarkin makera, waxanda ke shugabantar sanaoin bori [da bayar da magunguna na ciwuka], da farauta da su (kamun kifi da fito), da kuma qira. Dokaji(1958:7), ya ce, Barbushe shi ne shugaban da Kanawan wancan lokaci, suka zava, a matsayin sarkin fadan tsumburbura, wanda ke kula da jamaar da ke bautar wannan tsafi. Haka kuma, shi yake karvo saqo (daga tsumburbura zuwa ga jamaa), na duk abin da zai faru/auku a shekara, da abubuwan da ake son a yi. Da farko, a cikin sanaar farauta, mafarauci kan nuna gwanintarsa ta hanyar nuna iya kama wata dabba mai haxari, irin su zaki, da kura, da damisa,da maciji da sauran irinsu. Garba(1991:111), ya ce,a qasar Hausa, an san maharbi da yin sihiri da sanin yadda ake haxa wasu magunguna na61

aljanu da qarfe (wuqa da kibiya da mashi) da bindiga da duk wani dafi na namun daji. Yahaya(1992:59) kuwa cewa ya yi, maharba kan nuna qwarewarsu da bajintarsu ta hanyar bayar da maganin daji, da dafi, da kau-da-bara da sagau da xaurin dawa da fasa taro da waibuwar shashatau da banten biri da layar zana da ba-duhu da dai sauran irinsu. Yawancin waxannan dabaru ko sihiri, akan same su ne daga aljanu ko rauhanai, domin Garba(1991:112), ya ce, mai son yin farauta ko koyon farauta na iya tafiya gindin itaciyar kuka, wadda ake tsammanin tana da aljanu ko qwanqwamai, ya kwana a can, domin ya sami taimako daga gare su. Ita sanaar farauta, ita ce sanaar da ake sa ran, sanaa ce ta farko da Hausawa suka fara yi, da suka iso qasar Hausa. Ke nan, uwa ce mai bayar da mama, wadda daga gare ta ne yawancin sauran sanaoin Hausawa na gargajiya suka wanzu,hard a sanaar gardanci.Haka kuma daga gare ta ne suka sami dabarun tafiyar da sanaoinsu. Garba (1991 : 112), ya ce ana samun abubuwa da yawa daga wannan babbar sanaa ta farauta, wadda kuma ta daxe, tun lokacin da Allah Ya halicci xan Adam a duniya. Ita ce sanaar da mutum ya fara sani, kafin noma da saqa da xinki. Saboda haka, ana iya cewa, daga sanaar farauta ne wasu sanaoi na nuna sihiri da siddabaru da yin dabo da rufa ido da damfara da gwada waibuwoyi a cikin sanaoi, suka samo iliminsu na dabaru, a cikin sanaoinsu. Hausawa na cewa, barewa ba ta yin gudu, xanta ya yi rarrafe. Abin nufi shi ne, tunda daga sanaar farauta ne wasu sanaoi62

suka wanzu, saboda haka dole ne su wanzu tare da duk wasu aladu na sanaar farauta. Wannan shi ne ya sa ake ganin sanaar gardancin kuraye, da biri, da macizai, da kunami, duk sun wanzu ne daga sanaar farauta, kuma sun sami ilimin dabarun sihiri na sanaarsu daga sanaar farauta (Nasarawa,1997:9-12). Wannan zance lallai haka yake, domin idan mutum ya ga irin shigar da gardin wando da na dabbobi (kura, da biri, da maciji), ke yi, in zai yi wasa, kusan iri xaya ce da ta mafarauci(a duba rataye na goma sha takwas da na goma sha tara a ga shiga irin ta mafarauta). Alhassan(1982:46), ya ce, idan za a tafi farauta, akan yi shiri kamar za a yaqi, ta hanyar xaukar kare, da kuma tanadar qarfe, da baduhu, da kau-da-bara, da xamaru, da layu, da karhuna, da dagumma, da makamai iri-iri, don neman cin nasa, da kare kai, daga tsautsayi. Allahu Akbar! Ba ja, wai kare ya mutu a saura. Da ganin biri, lallai ya yi kama da mutum. Waxannan bayanai na irin shigar da mafarauta ke yi, iri xaya ce da wadda gardawan wando da na a-daki-buzu da kuma na dabbobi kan yi. Ke nan, ashe daman sanaar gardanci a qasar Hausa, sanaa ce mai alaqa da farauta. Wata sanaar, wadda take da hanyoyi na ban mamaki na gwada bajinta, a lokacin da ake gudanar da ita, ita ce sanaar fawa. Fawa sanaa ce ta rundanci, wadda ake yanka dabba, don a sayar da namanta ga jamaa (Alhassan,1982:51). Masu yin wannan sanaa ana kiransu da sunan mahauta (Yahaya,1982:56). Haka kuma, su ne ke gudanar da63

sanaar dambe. Su ma sukan je gindin itaciyar tsamiya, wadda ake sa ran tana da aljanu, don su nemi taimakon gudanar da sanaarsu (Madauci,1968:73). Hanyoyin nuna gwaninta a cikin wannan sanaa sun haxa da hawan qaho na dabba, da sanin asiran sarrafa dabba, da bayar da maganin dafin qaho, da qwarewa wajen yi dambe, da gwada tauri (Yahaya,1992:59). Ke nan, sanaar fawa da farauta, danjuma ne da danjummai, watau abokan juna ne. Daga farauta ne aka sami dabarun iya yanka dabba da fexar ta da sayar wa jamaa namanta. Bokaye su ne manyan malaman yan farauta da rundawa, waxanda su ne, a lokacin bikin buxar dawa, bayan mafarauta sun kama dabba ta farko a shekara, sai su kuma rundawa su fexe dabbar, su kuwa bokaye su yi duba na abubuwan da zai faru a wannan shekara (Galadanci,1982:81). Wannan duba ita ce ta ci gaba, har ya kasance gardawa na karatu kan yi ta har bayan da musulunci ya zo qasar Hausa. Hasali ma, malamai ne kan yanka duk wata dabbar da ake son ci a qasar Hausa, don yin koyi da wannan tsohuwar alada ta Hausawa. Sanaar noma babba ce a cikin sanaoin Hausawa na gargajiya, wadda take da hanyoyi barkatai na nuna gwanintar aiwatar da ita. Yahaya (1992:59), ya ce manoma na nuna gwanintarsu ta yin noma da daddare tare da aljanu, da yin sihiri na shuka hatsi ya fito a lokacin rani, da xaure gona, a nome ta a cikin lokaci qanqane. Haka kuma, sukan fitar da macizai bisa kunya, sukan xaure haxari ko a hana ruwan sama shiga64

gonar da ba a son ya shiga. Madauci (1968:75-77), ya qara da cewa, a lokacin bikin aikin gayya na noma, manoma kan gwada sihiri iri-iri. Sukan shiga cikin tulu, sukan murza kambu, sai zuma mai harbi ta fito, ko su riqa wuqa sai ta narke, ko su sanya qafarsu ta yi tsawo zalala, ko su mayar da mutane shanu, domin su yi kasin da za a sami taki ga gonar sarkin noma, da dai sauran irinsu. Lallai! Da ganin biri, ya yi kama da mutum. Ba shakka gardawan wando, ko dai daman manoma ne waxanda daga sanaar noma ne, suka vige, suka mayar da nuna sihiri da bayar da magunguna, a matsayin sanaa, ko kuma sun koyi ko sun sami siddabaru da suke yi daga manoma. Mallam Abdullahi Kangiwa ya ce, gardawan da ke zaune a Tungar gardawa (garin su gausu Mustafa, wanda gardi ne) da kuma garin Giwa-Ta-Zo (garin su qyanqyashe, wanda shi ma gardi ne na wando, kuma manomi ne) duk kusan manoma ne.12 Haba! Mutum ba ya aikin banza, wai biri ya ga iccen baba, ashe ba banza ba, marigayi qyanqyashe ya shahara a wajen wasannin gardanci, ashe shi ma manomi ne wanda yakan nuna gwanintar gardancinsa ta yin amfani da sihirin da ya koya a sanaar noma. Har ila yau, sanaar wanzanci na xaya daga cikin sanaoin gargajiya, da ake gwada gwaninta, ta qwarewa a cikinta. Wanzamai kan bayar da magungunan kaifi (na aska), da na valli-valli, da na waibuwa irin ta sarkin aska da mutanensa, kamar sakar wa mutum kuraje ko kureci12

Hirar Da Aka Yi Da Mallam Abdullahi Kangiwa, Shugaban Sashen Koyar Da Larabci, Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Sakkwato.

65

a kansa, ko lalacewar kaciya (Yahaya,1992:59). Haka kuma, a lokacin wasanninsu na wanzamai, sukan yi wasu wasannin asirai na rufa ido, kamar xura wa mutum gashi a ciki, da mayar da mutum mai kaciya, ya zama mai lova (watau marar kaciya) (Garba,1991:100). Wannan ya nuna cewa, gardawa, ba ma kamar na wando, mutane ne masu qwazo, domin kusan sun kalwaxe kowacce sanaa ta gargajiya, sun samo wani abu na sihiri, wanda suke yin amfani da shi a wajen gudanar da sanaarsu ta gardanci. Baya ga ya mayar da mutum, mai lova (bayan da yana da kaciya), gardawa kan iya sace wa mutum zakarinsa, ko su mayar da namiji ya mallaki farji irin na mata, ko kuma su mayar wa mace farjinta a gaban goshinta, da dai sauran irinsu. Wannan ya nuna, cewa, daga wajen wanzamai suka sami irin wanxannan laqunna.Ke nan gardawa suna da alaqa da sanaar wanzanci. Qira ma sanaa ce wadda Hausawa masu yinta kan gwada gwanintarsu, a cikinta, don nuna qwarewa da kuma fito da martabar sanaarsu a idon jamaa, tun kafin zuwan musulunci qasar Hausa. Garba (1991:44), ya ce, maqera sukan haxa da yin tsafi, a lokacin wasanninsu na gargajiya. Sukan yi wasa da wuta ta yadda sukan ga dama. Sukan ci wutar, da bakunansu, a garwashinta ko kuma a jikin qarfe. Shi kuwa Yahaya (1992 :59), cewa ya yi, maqera suna da qwarewa sosai a wajen iya sarrafa qarfe da rashin jin zafin wuta, ba ma kamar in ta qone su. Kuma, suna bayar da maganin qunar wuta ko wani dafi na qarfe. Rimmer66

(1948:118) ma, qara wa ya yi da cewa, maqera suna da juriya ainun a wajen jin zafin wuta, wadda ta kai har ba su kulawa da ita, in suna aikinsu da ita. Haka kuma, a lokacin wani biki nasu na suna ko aure ko bikin shekara na wasan wuta, sukan watsa wuta su yi ta wasa da ita a jikinsu, kamar masu jikin dutse. Amadun Rakatove ya ce, wannan sanaa ta qira suna yin ta ne domin su sharifai ne, jikokin Annabi, to amman buzaye (bugaje), sukan zo su yi bauta a wajen maqera, har su kai ga mallakar naqullan wuta.13 Shi ke nan, abin nema ya samu, wai matar direba ta hai fi taya, daman abin da muke so ke nan mu ji, cewa wasu mutane kan tafi wajen masu sanaoin gargajiya domin su koyi sanaar. Kuma daman ana ganin sanaar gardanci (ba ma kamar ta wando), kamar daga Zabarmawa (maqwaftan Buzaye) ta fito. Ke nan, lallai sanaar gardanci, sanaa ce wadda ta haxe kusan dukkan sanaoin Hausawa na gargajiya, domin ta zagaya cikin kusan kowacce sanaa, ta aro irin siddabarunta da irin magungunanta da kuma irin wasannin da akan yi a cikinta, don tallar magungunan. Wani mawaqi mai suna Hassan Wayam, a cikin wata waqa tasa mai suna Bakandamiya, yana cewa: Da bara da bara xan Mallam, Almajiri tsuntsu ne, In ya ji kukan tsaba, Ya yi fingi da kunne, Kama da mataccen kusu, Amma ba kusu ne ba, Mutum ne xan aljanna.Hirar Da Aka Yi Da Mallam Amadun Rakatave, Wakin Sarkin Maqera, Tsohuwar Kasuwa, Malumfashi.13

67

Abin nufi a nan shi ne, mutum (almajiri), in dai zai nemi ilimi (bara), to zai samu (ya zama xan aljanna). Wannan abu haka yake, a dangane da masu yin sanaar gardanci a qasar Hausa, domin sun kwantar da kansu (kamar yadda kusu ke yi), suka tafi yawo (kamar yadda tsuntsaye kan yi), suka yi barar ilimi daga sanaoi, kuma suka samu, suke yin amfani da shi, ga taimakon alummar Hausawa.Ke nan, siddabarun da gardawa kan nuna na bajinta,a lokacin sanaarsu ta gardanci,sun samo su ne daga sanaoin gargajiya na Hausa. Saboda haka, daga qarshe, ana iya cewa, tun kafin zuwan musulunci qasar Hausa, Hausawa suka yi fice ta hanyar nuna dabaru da qwarewa a cikin sanaar da mutum yake yi. Daga garesu ne ma, waxanda suka fi yin fice, sukan sami sarauta a cikin sanaarsu (Alhassan,1992:31). Haka kuma, kowacce sanaa ta gargajiya, a wancan lokaci, tana da wata hanya ta daban, irin tata, ta bayar da magani, don taimaka wa alummarta, da ke yinta, da kuma waxanda ba su yinta. A da can, kusan sirri ne mutum ya nuna irin asirai da siddabarorin da ya mallaka na waibuwa, sai dai kawai idan rana ta vaci, ko a lokacin da yake gudanar da sana'arsa, ko kuma lokacin da ake gudanar da wasu wasanni na samuwar wani abin farin ciki (biki), a gidansu ko a kasarsu. Alhassan(1982:39) ya bayyana cewa, masu gwada jaruntakar sanaarsu, a lokacin gudanar da sanaarsu, sun haxa da: wasan tauri, da dambe, da kokowa, da kwaraya da wasan68

farauta,da noma, da gardi na kura ko na maciji ko na kunama ko wasa da munumunu ko da wani abu irin waxannan Ke nan, daga neman nuna gwaninta da qwarewa, a cikin sanaoin Hausawa na gargajiya ne, masu sanaar gardanci na wando da na kura da na biri da na maciji da kuma na kunama, suka sami sila. Saboda haka, sanaar gardanci tana da alaqa ko dangantaka da sanaoin Hausawa na gargajiya tun kafin bayyanar musulunci a qasar Hausa, kamar yadda za mu ga bayanan da ke biye.

DANGANTAKAR 2.3 DANGANTAKAR SANAOIN HAUSAWA NA GARGAJIYA SANAAR GARDANCI DA SANAAR GARDANCI A QASAR HAUSA KAFIN ZUWAN MUSULINCI. Kamar yadda aka riga aka ga faruwar sanaoin gargajiya na Hausa, a qasar Hausa da kafuwar unguwanni a matsayin masanaantu (Naniya,1987:2) da kuma hanyoyin nuna gwaninta a cikin sanaoin gargajiya, yanzu kuma zamu ga yadda sanaar gardanci ta sami alaqa ko dangantaka da waxannan sanaoi, tun kafin zuwan musulunci qasar Hausa. Bahaushe mutum ne mai son halaye na nagarta, don haka yakan yi qoqarin tarbiyantar da yayansa ta hanyar koya masa irin sanaar da ake yi a gidansu ko unguwarsu. A sanadiyyar koya masa wannan sanaa ne, akan kuma koya wa da aladun wannan sanaa, wanda suka bambanta ta da wata sanaar (Alhassan,1982:31). Koyon sanaa, yana bin gado ne. Sai69

xan gado ko wanda ya bauta wa sanaa ne a kan sanar da shi asirran da ke cikin sanaa. Idan wani mai sanaa ya tafi wani baqon gari, yakan nemi ya sauka a gidan mutanen da suke yin irin sanaarsa, don tsaron mutunci. Idan ma koyon sanaa mutum ya tafi a wani gari, to, yakan nemi ya je gidan abokan sanaarsa ne (Alhassan,1982:7 da 31). Ke nan, wannan ya nuna cewa, tun kafin zuwan musulunci, Hausawa suna da wayewar kai irin tasu(Ibrahim,1982:117). To, lokacin da Hausawa suka fara yawa, kuma suka sami cuxanya da wasu qabilu, irin su Auzinawa da Adarawa da Buzaye, sai wasu baqin aladu suka rinqa shigowa qasar Hausa (Galadanci,1992:32). Wannan ne ya sanya ake jin cewa, sanaar gardanci, sanaa ce baquwa, wadda Bahaushe ya koya daga Zabarmawa.14 Haka ma Galadanci (1992 : 33) da Dokaji(1958:3), duk sun yarda da cewa, cuxanya da baqi da Hausawa suka yi ta haifar da ko ta haddasa shigowar wasu baqin aladu cikin qasar Hausa, irin su yan sace-sace da fashi da kai hare-hare da satar mutane, wanda a da duk ba su yi, in baya ga rikon aladunsu na gado (Alhassan,1982:6-7). To, amman da yake Bahaushe hankaka ne, mai mayar da xan wani nasa, wanda tun fil'azal ya yarda da koyon sana'ar wani, domin ya gyara ta, ya mayar da ita tasa, ta hanyar yin bauta ko barantaka (Alhassan,1882:8), sai aka sami wasu waxanda suka mayar da gwada gwanintar sana'o'in gargajiya, a matsayin sana'a. Irin waxannan14

Hirar Da Aka Yi Da Mallam Hamisu Abdullahi Beta, Xa